Shekarau zai canji Kwankwaso a majalisar dattijai

Shekarau zai canji Kwankwaso a majalisar dattijai

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau na jam'iyyar APC ya yi nasarar lashe kujerar sanata ta tsakiya.

Kamar yadda sakamakon zaben ya nuna, Shekarau ya samu kuri'u 506,276 ne inda ya kayar da babban abokin hammayarsa na jam'iyyar adawa ta PDP Ali Madaki da ya samu kuri'u 29,775.

A yayin da ya zanta da Bbc bayan hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben, Shekarau ya ce shine sanata da yafi dukkan sauran samun kuri'u a Najeriya.

DUBA WANNAN: Zabe: Sakamako daga jihohin Sokoto, Kebbi da Jigawa

Shekarau zai canji Kwankwaso a majalisar dattijai
Shekarau zai canji Kwankwaso a majalisar dattijai
Asali: Depositphotos

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa dukkan 'yan takarar sanata uku a jihar Kano sunyi nasarar lashe zabensu.

Sauran 'yan takarar biyu dama sune suke kan kujerar sanatan a yanzu.

Sanatocin biyu sune Sanata Kabiru Gaya mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu sai kuma Sanata Barau Jibril-Maliya da ke wakiltar mazabar Kano ta Arewa kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel