Shekarau ya gana da Kwankwaso bayan sulalewar sa daga APC zuwa PDP

Shekarau ya gana da Kwankwaso bayan sulalewar sa daga APC zuwa PDP

Labarin da ke zuwa mana shi ne an yi wani zaman kus-kus a cikin daren nan tsakanin manyan ‘Yan siyasar Jihar Kano watau Malam Ibrahim Shekarau da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya bar Jam’iyyar APC kwanaki.

Shekarau ya gana da Kwankwaso bayan sulalewar sa daga APC zuwa PDP
Kwankwaso da Shekarau. Hoto daga: Hon Saifullahi Hassan

Tsofaffin Gwamnonin Jihar sun yi wani zama ne a babban Birnin Tarayya Abuja a jiya cikin dare. Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya samu tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau a gidan su su ka tattauna.

A cikin makon jiya ne tsohon Gwamnan na Kano Rabiu Kwankwaso ya tsere daga Jam’iyyar APC. Kwankwaso ya dawo tsohuwar Jam’iyyar sa ne ta PDP bayan ya samu sabani da Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

Shekarau ya gana da Kwankwaso bayan sulalewar sa daga APC zuwa PDP
Shekarau ya gana da Kwankwaso bayan sulalewar sa daga APC zuwa PDP

Ana ta rade-radin cewa Ibrahim Shekarau ba zai iya aiki da Rabiu Kwankwaso ba saboda irin halin sa na siyasa. Don haka ne APC ta fara shirin raba Shekarau da Kwankwaso domin ganin Jam’iyyar adawar ta samu rauni a Kano.

KU KARANTA: An gano cewa mai neman Gwamna bai yi karatu ba

Tuni dama dai tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya tabbatar da cewa ba zai fice daga Jam’iyyar PDP ya koma APC ba. Shekarau ya koka da rashin adalcin Jam’iyyar APC wanda yace shi ya sa shi ma Kwankwaso ya bar ta.

Shekarau ya gana da Kwankwaso bayan sulalewar sa daga APC zuwa PDP
Kwankwaso da Shekarau. Hoto daga: Hon Saifullahi Hassan

Kawo yanzu dai babu wanda ya san abin da manyan ‘Yan siyasar su ka tattauna. Ana sa rai dukkan su za su nemi takarar Shugaban kasa a 2019. Shekarau yayi takara a ANPP a 2011 inda Kwankwaso ya jarraba sa’a a 2015.

Ku na da labari cewa a cikin ‘Yan Majalisar Wakilan da su ka bar APC su ka koma PDP akwai wasu mutum 10 daga Kano. ‘Yan Majalisar Tarayyan sun bi tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel