Fayose: Zan kalubalanci Makinde idan ya taba shugabancin PDP na yankin Kudu

Fayose: Zan kalubalanci Makinde idan ya taba shugabancin PDP na yankin Kudu

Ayodele Fayose, tsohon gwamnan Ekiti, ya ce zai kalubalanci Seyi Makinde na jihar Oyo, muddin ya yi gigin taba shugabancin PDP a jiharsa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar The Cable a ranar 9 ga watan Satumba, tsohon gwamnan ya gargadi gwamnan Oyo mai-ci, Seyi Makinde.

Mista Ayodele Fayose ya ja kunnen Makinde ne a lokacin da ya jagoranci shugabannin jam’iyyyar PDP zuwa garin Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Laraba.

Wadanda Fayose ya yi tafiya da su, su ne shugabannin PDP na jihohin kudu maso yamma, Deji Doherty (Legas), Sunday Akanfe (Osun), da Bisi Kolawole (Ekiti).

KU KARANTA: PDP da APC za su goge raini wajen lashe kujerun Majalisar dattawa

A cewar tsohon gwamnan, Makinde bai da ikon da zai yi wasa da shugabancin PDP na jihohin yankin, duk da ya na cikin jagororin jam'iyya a Kudancin Najeriya.

Fayose ya ce shugabannin jam’iyyar PDP ne su ke da alhakin jan ragamar jam’iyya a mazabunsu.

Kamar yadda tsohon gwamnan na Ekiti ya bayyana, Seyi Makinde ya bada umarnin a sauke shugabannin PDP na shiyyoyi, a maye gurbinsu da ‘yan rikon-kwarya.

Mista Fayose ya ce ba zai yarda da yunkurin taba shugabannin PDP na jihar Ekiti ba.

“Ana yaki a boye a kan wadanda za su shugabanci PDP a shiyyar Kudu maso yamma. Gwamna Makinde ya bukaci a sauke daukacin shugabannin shiyyoyi.” Inji Fayose.

KU KARANTA: Ayo Fayose ya ji dadin cafke Magu da binciken da ake yi a kansa

Fayose: Zan kalubalanci Makinde idan ya taba shugabancin PDP na yankin Kudu
Ayo Peter Fayose Hoto: This Day
Source: Instagram

Sannan Ayo Fayose ya kara da cewa, “(Makinde) ya bada umarni a nada shugabannin rikon kwarya a yankin, wanda kuma jam’iyya ta yi.”

‘Dan siyasar ya dada da: “Amma tun daga lokacin da aka kafa kwamitin rikon kwarya, bai bar su sun yi aiki ba domin shi ne ya fito da shugaba.”

Bayan duk wannan, Fayose ya ce babu dalilin da za a ce ba zai shiga wata jiha ba, ya ce ‘Zan cigaba da ganin girmansa, ina cikin wadanda su ka yi sanadiyyar zamansa (Makinde) gwamna.”

A karshen zaman da aka yi, shugabannin PDP sun sa hannu tare da shugaban jam’iyya na jihar Ogun, Sikirullahi Ogundele.

Ku na da labari cewa ana rigima tsakanin Ayo Fayose da Sanata Biodun Olujumi a jihar Ekti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel