Bayan dadewa babu duriyar Mamman Daura, ya je ta'aziyya Adamawa

Bayan dadewa babu duriyar Mamman Daura, ya je ta'aziyya Adamawa

- Bayan kwashe tsawon lokaci ba a jin duriyar Mamman Daura, ya ziyarci jihar Adamawa domin ta'aziyyar Dr Mahmud Tukur

- Makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance shakikin abokin marigayi Dr Mahmud Tukur

- Ya kwatanta mamacin da mutumin da kofarsa ta taimako bude take ga kowanne dan Najeriya ba tare da duban banbanci ba

A daya daga cikin fitarsa ta musamman a 2021, dan uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma makusancinsa, Mamman Daura, ya ziyarci jihar Adamawa saboda rasuwar abokinsa, Dr Mahmud Tukur.

A ta'aziyyar da ta dinga bayyana ta rasuwar Tukur, an dinga bayyana kusancinsa da Mamman Daura.

Yayin da ya ziyarci Gwamna Ahmadu Fintiri a ranar Lahadi, Daura ya kwatanta marigayi Tukur da abun koyi kuma jigo a kasar nan wanda a koyaushe kofarsa bude take ga 'yan Najerita ba tare da duban wani banbanci ba.

Daura ya sanar da cewa Tukur mutum ne mai dabi'a ta gari, ilimi, mutunci kuma babban misalin dan kasa nagari wanda a koyaushe yake fatan ganin hadin kan 'yan Najeriya.

KU KARANTA: OPC, IPOB da Boko Haram duk abu daya ne, babu banbanci, Dambazau

Bayan dadewa babu duriyar Mamman Daura, ya je ta'aziyya Adamawa
Bayan dadewa babu duriyar Mamman Daura, ya je ta'aziyya Adamawa. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude

masallacinsu

A yayin da Fintiri ke godiya ga Daura a kan yadda ya nuna kauna, ya ce Tukur ya mayar da hankali wurin bautawa kasarsa ta gado.

Ya kara da cewa mutuwarsa a wannan lokacin da kasar nan ke habaka tare da fuskantar kalubale ya zama babban abu.

An haifi Mahmud Tukur ne a shekarar 1939 a garin Yola, jihar Adamawa. Marigayin ya rasu kenan ya na da shekara 82 a Duniya.

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace ba zai baiwa wani mai garkuwa da mutane ko sisi ba koda kuwa dansa ne yake hannunsu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hirar gidan rediyo da aka yi dashi ranar Juma'a akan yadda gwamnatinsa take bullo wa 'yan bindiga, Premium Times ta ruwaito.

El-Rufai ya dade yana bayyana yadda yake amfani da karfi wurin magance ta'addanci a jiharsa, kuma yana tsaye akan bakarsa. Ya maimaita a ranar Alhamis cewa babu wani dan ta'adda daya dace ya rayu a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel