Danne nasarar Abiola a 1993: Obasanjo na da hannu ciki - Babagana Kingigbe

Danne nasarar Abiola a 1993: Obasanjo na da hannu ciki - Babagana Kingigbe

Abokin tafiyar marigayi, MKO Abiola a zaben 12 ga Yunin 1993, Babagana Kingigbe, ya bayyana cewa yana da faifan bidiyon abubuwan da suka shafi zaben da tsohon shugaba Ibrahim Babangida ya danne.

Kingigbe ya bayyana hakan ne a wani hira da ya gabatarwa gidan talabijin NTA ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, 2019.

Tsohon sakataren gwamnatin ta dade yana shan sukan cewa bai cikin wadanda sukayi gwagwarmayan kwato hakkin Abiola bayan Janar Babangida ya soke zaben bisa wasu dalilai maras isnadi.

Babagana Kingigbe ya kasance ministan harkokin wajen Najeriya a gwamnatin Abachar da ta daure abokinsa Abiola. Hakan ya sa jama'a suke yi masa kallon mayaudari.

KU KARANTA: Shegiyar uwa: Wata mai jego ta gudu ta bar jaririyarta a asibiti

A hirar, ya bayyana cewa tsawon shekaru ya ki magana kan al'amarin saboda idan ya yi magana, zai shafe maganar wasu a kai.

Yace: "Wannan shine karo na farko da zanyi magana kai. Wani zubin abin kan daure min kai amma ba na mamakin maganganun mutane kan wadanda sukayi gwagwarmayan 12 ga Yuni."

"Na san dukkan abinda ya faru kuma babu yadda mutum zai yi fadi gaskiya kan ranar 12 ga Yuni ba tare da shafe na wasu ba."

"Ina da ajiyayyen tarihin abubuwan da suka faru ranar. Ina sa ran cewa zan samu damar fadin nawa labarin wata rana. Faifan bidiyo ne, ba rediyo ba."

Kingigbe yace, tsohon shugaban kasa Obasanjo na daga cikin ummul haba'isin soke zaben, duk da cewa daga baya ya yi nadama.

Yace: "Bayan soke zaben, daya daga cikin ummul haba'isin sokewa, tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya yi kokarin hada kan wasu manya domin shawo kan al'amarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel