‘Ya ‘Yan Abiola da Yaran gidansa sun samu ‘yanci daga hannun ‘Yan Sanda

‘Ya ‘Yan Abiola da Yaran gidansa sun samu ‘yanci daga hannun ‘Yan Sanda

- Ana kishin-kishin din cewa ‘Yan gidan Abiola da ke tsare sun samu ‘yanci

- Kwanakin baya aka kama Yaran gidan Marigayin bayan an shiga an yi fashi

- Wata ‘Diyar Abiola ta karbo belin ‘Yanuwan na ta daga hannun ‘yan sanda

Dakarun ‘yan sandan jihar Legas sun saki wasu ‘ya ‘ya biyu daga cikin iyalin marigayi Moshood Kasimawo Olawale Abiola da ke tsare a hannunsu.

Jami’an tsaron sun tsare ‘ya ‘yan marigayin da wasu ma’aikatan gidansa uku bisa zarginsu da laifin hannu a fashin da aka yi a gidan MKO Abiola kwanaki.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa an shigar da karar wadannan mutane da ake zargi da laifi a karamin kotun majistare da ke Ogba, a jihar Legas.

KU KARANTA: Ba ni na kashe Kudirat Abiola ba - Hamza Almustapha

Rahoton ya bayyana cewa ana tuhumarsu ne da laifin hada-kai wajen tafka barna, sata, kutsawa gidan mutane da wasu laifuffukan masu kama da juna.

Ma’aikatan da ake zargi da hannu a fashin gidan wannan Bawan Allah sun hada har da hadiminsa, mai gyaran lambu da kuma mai sukola da guga na gidan.

Daga baya babbar ‘diyar marigayin, Honarabul Lola Abiola-Edewor, ta tsayawa ragowar ‘yanuwanta da ma’aikatan gidansu, ta nemi a bada belinsu.

Da kimanin karfe 3:30 na ranar 15 ga watan Satumba, an ga wannan mata ta na kokarin kubuto da wadanda ke tsaren daga hannun jami’an ‘yan sanda na Legas.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun yi ram da wani gawurtaccen 'dan fashi da makami

‘Ya ‘Yan Abiola da Yaran gidansa sun samu ‘yanci daga hannun ‘Yan Sanda
Marigayi MKO Abiola Hoto: This Day
Source: UGC

Da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar, SP Muyiwa Adejobi, ya gagara yin magana game da lamarin, ya ki cewa uffan domin har yanzu ana kan bincike.

Idan za ku iya tunawa, mutum tara jami’an ‘yan sanda su ka kama bayan an kutsa gidan tsohon ‘dan kasuwar nan, MKO Abiola da ke Ikeja, jihar Legas.

A dalilin haka wasu ‘ya ‘ya biyu na marigayin su ka shigar da kara a kotu, su na bukatar ‘yan sanda su biya su Naira miliyan 100 na keta masu alfarma da aka yi.

Ana zargin cewa an yi awon gaba da makudan kudi a lokacin da aka shiga gidan MKO Abiola.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel