2023: Maganar takarar Tinubu ta kara kaimi, Magoya-baya sun fara bude ofisoshin kamfe

2023: Maganar takarar Tinubu ta kara kaimi, Magoya-baya sun fara bude ofisoshin kamfe

- Kungiyar SWAGA 23 ta shiga jihar Ondo, ta bude sabon ofis domin yakin zabe

- Ifedayo Abegunde aka zaba ya yi wa Bola Tinubu yakin neman zabe a Ondo

- Bayan haka wasu magoya bayan ‘Dan siyasar sun fito da tafiyar BAT a Legas

Masoya da magoya-bayan jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, sun kaddamar da wani sabon ofishin kungiyar SWAGA 23 a jihar Ondo.

Jaridar nan ta Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Juma’a, 9 ga watan Afrilu, 2021.

Kungiyar SWAGA 23 watau South West Agenda for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta na yi wa Bola Tinubu yakin neman zaben shugaban kasar Najeriya.

KU KARANTA: Jagoran Afenifere, Reuben Fasoranti ya na tare Bola Tinubu

Da ake bude ofishin SWAGA 23 a Ondo, shugaban wannan tafiya, Sanata Dayo Adeyeye, ya ce kungiyar za ta ratsa duka kananan hukumomi 18 na jihar.

Sanata Dayo Adeyeye wanda ya rike Ministan ayyuka a gwamnatin tarayya ya ce burinsu shi ne kungiyar SWAGA ta karade jihohin Kudu maso yamma.

Kamar yadda Dayo Adeyeye ya bayyana, SWAGA ta na kokarin ganin tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Tinubu ya gaji shugaba Muhammadu Buhari.

Mista Ifedayo Abegunde ne aka nada a matsayin sabon shugaban kungiyar SWAGA 23 a jihar Ondo.

2023: Maganar takarar Tinubu ta kara kaimi, Magoya-baya sun fara bude ofisoshi
Jigon APC, Bola Tinubu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kungiyar Afenifere ta musanya cewa tana tare da Tinubu

Ifedayo Abegunde ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu bai ce zai yi takara a 2023 ba, su ne kurum su ke fafutuka domin ganin ya nemi mulkin kasar nan.

“Mu ne mu ke dakon wannan aiki da wasu ‘yan kishin-kasa irinmu su ke mara mana baya.” Inji Abegunde.

A daidai wannan lokaci ne kuma ‘dan majalisar Legas, Hon. Gbolahan Yishawu, ya kaddamar da tafiyar Bola Asiwaju Tinubu (BAT) duk a cikin shirin zaben 2023.

Kwanakin baya kun samu labari cewa takarar Bola Ahmed Tinubu ta na samun karbuwa sannu a hankali a wajen Sarakunan Yarbawa ta hannun kungiyar SWAGA 23.

Asali: Legit.ng

Online view pixel