Ba zamu zuba ido muna Kallo ana kashe mana Mutane a Kudu ba, Sanata Babba kaita ya yi kakkausan Gargaɗi
- Sanata Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina ya yi kakkausan gargaɗi ga yan kudancin ƙasar nan kan yawan kashe-kashen da ake samu na yan arewa a yankin su
- Sanatan yace shiru ba tsoro bane kuma su sani yan arewa sun iya buga wasan
- Sanatan wanda ya fito daga mazaɓar sanatan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fito, ya ce yanzun babban laifin da zakai shine kazama ɗan arewa dake zaune a kudu
Sanata Ahmad Babba Kaita, wanda ke wakiltar mazaɓar Katsina ta arewa ya yi kira da a dakatar da kashe yan arewa a kudancin ƙasar nan cikin gaggawa.
Sanatan ya ce babu yankin dake son tashin hankali kamar yadda jaridr Dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yanzu Yanzu: El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru
Sanata Kaita, wanda ya fito daga yankin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake, ya ce kamar dai yan kudancin ƙasar nan, yakamta abar kowane ɗan arewa ya yi rayuwa cikin kwanciyar hankali.
Kuma yakamata abarsu su yi kasuwancin a kudanci kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya tanada.
Idan zaku iya tunawa, kwanakin baya, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya gargaɗi yan kudancin ƙasar nan dake rayuwa a arewa da kada su yi tsammanin kariya matuƙar aka cigaba d kashe yan arewa a kudu.
Sanata Babba Kaita a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi ma take 'Arewa: babu sauran yin shiru' ya ce a yanzun babban laifin ka shine ka zama ɗan arewa.
KARANTA ANAN: Da dumi-dumi: Rikici ya barke a gidan yarin Bauchi, mutum 7 sun jikkata
Kaita ya ce:
"Dan kogi yi tsaya cak, bashi ke tabbatar da cewa babu kadoji a ƙarƙashinsa ba, kamar haka ne dan ana cin mutuncin arewa ta hanyoyi da dama kuma mun yi shiru, hakan ba yana nufin yan arewa ba su iya ramuwar gayya bane ko kuma basu san yadda ake buga wasan ba."
Sanatan wanda yana goyon bayan kujerar shugaban ƙasa ta koma kudu a zaɓen 2023 ya ce yan arewa sun yi shiru ne don kawai Najeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya.
Amma Kaita yace kowa ya yi da kyau to fa nan gaba shima zaiga dakyau, babu mai tantama akan wannan.
Ya ƙara da cewa a ko ina a faɗin duniya, gina ƙasa ba aikin mutum ɗaya bane, dole sai kowa ya bada haɗin kai, kuma Najeriya wani ɓangare ne na duniya.
A wani labarin kuma 'Yan Boko Haram sun sace mata 30 bayan kashe mutum biyar a Adamawa
'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyen Kwapre da ke jihar Adamawa
Sun halaka mutane guda biyar sannan sun yi awon gaba da mata a kalla guda 30 bayan lalata gidaje da dukiyoyi.
Asali: Legit.ng