Buhari: Yadda uwargidata, Aisha, ta inganta rayuwar yan Najeriya

Buhari: Yadda uwargidata, Aisha, ta inganta rayuwar yan Najeriya

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alheran da mai dakinsa ke yiwa yan Najeriya

- A ranar Alhamis, an kaddamar da sabon littafin kan rayuwar Aisha Buhari, mai dakin shugaban kasa

- Buhari ya siffanta Aisha a matsayin mai tausayin talakawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin yadda uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari, ta taimakawa rayuwar yan Najeriya ta hanyoyi daban-daban.

A jawabin gabatarwa da yayi a sabon littafinta da aka kaddamar ranar Alhamis kuma bai samu halarta ba, Buhari ya ce wannan littafin ya bashi daman fadin wasu kalamai akan uwargidarsa.

Ya ce Aisha, karkashin shirinta na 'Future Assured' ta na cika burinta na taimakawa talakawa, marasa lafiya da marasa galihu har a karkara.

Ya kara da cewa tayi matukar taimakawa mata, kananan yara da kuma marasa karfi cikin al'umma.

KU KARANTA: An samu matsaya tsakanin Likitoci da Gwamnati, da yiwuwan zasu janye yajin aiki yau

Buhari: Yadda uwargidata, Aisha, ta inganta rayuwar yan Najeriya
Buhari: Yadda uwargidata, Aisha, ta inganta rayuwar yan Najeriya Credit: Presidency

KU KARANTA: Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

"Aisha kamar yadda aka sani mutum ce mai kirki; hakan ya sa taimakawa al'umma yayi mata sauki lokacin da ta zama uwargidar shugaban kasa. Ta fi bayar da karfi wajen kare rayuwar mata, yara da marasa karfi," Buhari yace.

"Na lura da cewa ta magance matsalolin jin dadin rayuwa cikin jama'a da ya dade yana mata takaici."

"Shirinta na 'Future Assured' ya bata daman cimma burinta na taimakawa talakawa, marasa lafiya, marasa karfi a karkara, musamman sansanin yan gudun Hijra."

Buhari ya ce dukkan wadannan abubuwan da take yi ya inganta rayuwar yan Najeriya, shiyasa ake alfahari da kasar da kuma kasancewarta abokiyar huldarsa.

A bangare guda, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana kaunar mutanen Ogbia, wata karamar kabilar Ijaw a cikin jihar Bayelsa.

Ministan ya ce dalili kuwa daya ne, saboda dansu, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya bar masa mulki cikin lumana a 2015, The Nation ta ruwaito.

Sylva ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya ke duba aikin da ake yi na samar da Man Fetur da Gas na Kasa (NOGaPS) wanda Hukumar NCDMB ke ginawa a Emeyal 1, karamar hukumar Ogbia ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel