Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP 11 sun dira Makurdi domin hallartar taro

Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP 11 sun dira Makurdi domin hallartar taro

- Gwamnonin jihohin babban jam'iyyar hamayya ta PDP sun isa garin Makurdi, jihar Benue

- Dr Samuel Ortom, mai masaukin baki ya tafi filin tashi da saukan jiragen sama na Makurdi ya tarbe su

- Majiyoyi sun ruwaito cewa abinda gwamnonin za su mayar da hankali kai shine tsaro da babban zaben 2023

An kammala shiryawa tsaf domin yin taron kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a garin Makurdi babban jihar Benue, Vanguard ta ruwaito.

Mai masaukin baki, Dr Samuel Ortom, cikin awanni da suka gabata ya tarbi takwarorinsa a filin sauka da tashin jirage na Makurdi d suka zo taron.

DUBA WANNAN: An tsinci gawarwakin sojoji 11 da 'yan bindiga suka kaiwa hari a Benue

Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP 11 sun dira Makurdi domin hallartar taro
Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP 11 sun dira Makurdi domin hallartar taro. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

A lokacin hada wannan rahoton, Nyesome Wike na jihar Rivers, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da Ifeanyi Okowa na jihar Delta suna dakin taro na gidan gwamnatin jihar Benue inda za a yi taron.

Saura sun da suka isa Makurdi sun hada da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Adamu Fintiri na jihar Adamawa, Duoye Diri na jihar Bayelsa, Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom da Darius Ishaku na jihar Taraba.

KU KARANTA: Tinubu ya ziyarci Buni domin yi masa ta'aziyar rasuwar Hajiya Fatima Yuram

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tella shima yana gari; alama da ke nuna mai gidansa, Bala Mohammed ba zai samu ikon zuwa ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa abin da ake sa ran tattaunawa wurin taron shine kallubalen tsaro a kasar da kuma lafiyar jam'iyyar PDP da shirye-shiryen babban zaben shekarar 2023.

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel