Sarkin Zazzau ya nada Shehu Tijjani matsayin sabon Ciroman Zazzau

Sarkin Zazzau ya nada Shehu Tijjani matsayin sabon Ciroman Zazzau

- Ba tare da bata lokaci ba, an nada sabon Ciroman Zazzau

- Har yanzu, sabon Sarkin Zazzau na cigaba da fuskantar kalubale daga cikin 'yan majalisarsa

- Hakan ya sa ta kwancewa daya daga cikinsu rawani a makon nan

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi karin girma ga Mallam Shehu Tijjani Alu Dan Sidi Barden Zazzau zuwa Ciroman Zazzau.

Wannan ya biyo bayan kwance rawanin tsohon Ciroman Zazzau, Alhaji Sai’du Mai Lafiya.

Sarkin ya tube rawanin Ciroman Zazzau ne saboda zargin rashin biyayya da girmama masarautar.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta saki hotuna da sunayen Fursunonin da suka gudu a Owerri

Sarkin Zazzau ya nada Shehu Tijjani matsayin sabon Ciroman Zazzau
Sarkin Zazzau ya nada Shehu Tijjani matsayin sabon Ciroman Zazzau
Asali: Facebook

KU KARANTA: Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri

A ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2020, Ahmed Nuhu Bamalli ya gaji Alhaji Shehu Idris a kan karagar Sarkin Zazzau.

Cikin yan watannin da yayi kan karagar mulki, an samu sauye-sauye da dama a masarautar Zazzau

Ga kadan daga cikin sauye-sauyen:

1. Yi wa gidan Bare-bari babban nadi

2. Karbe sarautar Iyan Zazzau daga gidan Katsinawa zuwa na gidan Abbas Tajuddeen na Mallawa.

3.Magajin Garin Zazzau

Sabon sarki ya bada sarautarsa ta Magajin Gari ga ‘danuwansa, Mansur Nuhu Bamalli. Mai martaba ya tsallake mai bi masa a gidan Nuhu Bamalli, ya dauko Barde Kerarriya.

4. Maye gurbin wadanda suka rasu

Bayan Iyan Zazzau, Ahmed Bamalli ya nada sababbin Sa’i da Talban Zazzau bayan rasuwar wadanda su ke rike da wannan mukamai. Talba ya koma gidan Iya Bashar Aminu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel