Abubuwan da Yusuf Buhari ya fada a game da Aisha Buhari a sabon littafinta ‘Being Different’
- Yusuf Buhari ya yi magana game da mahaifiyarsu, Hajiya Aisha Buhari
- An tsakuro maganarsa ne a littafin da aka rubuta a kan tarihin rayuwar ta
- Yusuf ya bayyana cewa tsohuwarsu ta yi masu komai a rayuwar Duniya
Yusuf, ‘dan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin jajirtacciya.
Uwargidar shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Muuhammadu Buhari ta yi fice wajen fadin duk abin da ke ran ta, ba tare da tsoron abin da zai biyo ba.
A wajen kaddamar da littafin da aka rubuta na “Aisha Buhari: Being Different” a kan tarihin tsohuwarsa, Yusuf ya bayyana wacece mahaifiyarsu.
KU KARANTA: Aisha Buhari ta sha banbam da sauran matan Shugabanni - Osinbajo
Yusuf Buhari wanda shi kadai ne ‘dan shugaban kasa, ‘yanuwansa duka mata ne, ya bada labarin irin dankon da ke tsakaninsa da mahaifiyar ta su.
Daily Trust ta rahoto Yusuf Buhari ya na cewa bai isa ya yi wani abu a rayuwa ba tare da ya sanar da mahaifiyarsa, Aisha Muhammadu Buhari ba.
Amma duk da haka, Malam Yusuf Buhari ya ce wani lokacin ya kan yi watsi da batun mahaifiyarsa, ya je ya aikata abin da ba ta amince ba.
“Ta na da matukar soyayya da kauna, ina kiranta Dakta, daktan da bata karanci ilmin likitanci ba. Ta na maganin kowace matsala mutum yake da ita.”
KU KARANTA: Wadanda su ka yi ruwan kudi wajen bikin bude littafin Aisha Buhari
Ya cigaba: “Ta na da magani nan-take a kan duk abinda ka kawo mata. Ta na da ban dariya, jajirtacciya, wanda ka da ka sake ka samu sabani da ita.”
“Ba ta ja da baya har sai ta ga karshen lamura. Ta na fadan duk abin da ya ke cikinta, kuma ta tsaya tsayin-daka a kai.” Inji Yusuf Buhari a cikin littafin.
Dazu kun ji cewa Mai dakin tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ta amsa gayyatar Aisha Buhari, ta halarci bikin kaddamar da littafin da aka yi.
Taro ya yi taro, amma shugaban kasa Muhammadu Buhari bai samu damar halarta ba domin ya na kasar Ingila inda manyan Likitoci su ke duba lafiyar jikinsa.
Asali: Legit.ng