Osinbajo: Inda Aisha Buhari ta sha banbam da Matan Shugabannin kasa da aka yi a tarihi

Osinbajo: Inda Aisha Buhari ta sha banbam da Matan Shugabannin kasa da aka yi a tarihi

- Farfesa Yemi Osinbajo ya yabi Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari

- Yemi Osinbajo ya ce ba a taba ganin uwargidar shugaban kasa irinta ba

- Mataimakin shugaban kasar ya ce ba za a manta da Aisha Buhari ba

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana Hajiya Aisha Buhari da matar da ta canza salon ofishin uwargidar shugaban kasa.

Jaridar The Nation ta rahoto Farfesa Yemi Osinbajo ya na cewa Aisha Muhammadu Buhari mata ce wanda ta sha dabam da duk sauran takwarorinta.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Yemi Osinbajo ya ce Aisha Buhari ta sha banbam da sauran matan shugabannin kasan da aka yi a tarihin Najeriya.

KU KARANTA: Tinubu ya bugi galan wajen kaddamar da littafin Aisha Buhari

A cewar Osinbajo, dabi’ar Hajiya Aisha Buhari ne ya jawo mata farin-jini wajen al'ummar Najeriya.

Osinbajo ya ce daga cikin inda Aisha Buhari ta banbamta da sauran matan shugabannin da aka yi a baya shi ne ta bude shafukan sada zumunta a kafafen zamani.

“Da wahala a ce an yi wata uwargidar shugaban Najeriya a baya wanda a cikin kankanin lokaci ta shiga zuciyar mutane sosai kamar Aisha Buhari.” Inji Osinbajo.

“Ita ce uwargidar shugaban Najeriyar farko da aka gani a shafin Twitter, Instagram da sauran dandalin sada zumunta na zamani, kuma aka san da zamanta.”

KU KARANTA: Wadanda su ka bada kudi wajen bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari

Osinbajo: Inda Aisha Buhari ta sha banbam da Matan Shugabannin kasa da aka yi a tarihi
Bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari
Asali: UGC

Osinbajo yake cewa: “Kuma watakila ita ce ta farko da ta ke samun ra’ayoyin ‘Yan Najeriya kai-tsaye.”

“Da ra’ayoyinta na kai-tsaye da fadan gaskiya da wasu ke ganin sun sha banbam wasu lokutan, ta jawo abin magana wajen ‘Yan Najeriya da har yau ba a daina ba."

Mataimakin shugaban kasar ya ce Uwargidar mai gidansa ta fita dabam a dalilin taimakon jama’a da ta ke yi, ya ce za a dade ba a manta da ita a tarihin kasar nan ba.

Mai girma mataimakin shugaban Najeriyar ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin kaddamar da littafin da aka rubuta a game da mai dakin shugaban kasa dazu.

Kun ji cewa kaddamar da sabon littafin tarihin na Aisha Buhari ya jawo ana ta surutu a dandalin Twitter, har wasu su na cewa kudi uwargidar Najeriyar ta ke nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel