Wata sabon gani: Dame Jonathan da Orubebe sun halarci bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari

Wata sabon gani: Dame Jonathan da Orubebe sun halarci bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari

- An kaddamar da littafin rayuwar Uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Buhari

- Mai dakin tsohon shugaban kasa, Mrs. Patience Jonathan ta samu halartar taron

- Mutane sun yi mamakin ganin jigon PDP, Elder Godsday Orubebe a Aso Villa

A ranar Alhamis, 8 ga watan Afrilu, 2021 ne aka kaddamar da littafin da Dr. Hajo Sani ta rubuta a game da rayuwar Hajiya Aisha Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta ce tsohuwar uwargidar Najeriya, Dame Patience Jonathan, ta na cikin wadanda su ka halarci bikin kaddamar da littafin matar da ta gaje ta.

Jaridar ta ce an ga tsohon Ministan harkokin Neja-Delta, Elder Godsday Orubebe a wajen wannan biki.

KU KARANTA: Yadda na yi fama da auren wuri a gidan Buhari - Aisha Buhari

Mista Elder Godsday Orubebe rikakken ‘dan a-mutun tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ne wanda ya kusa kawo matsala a lokacin zaben 2015.

Godsday Orubebe ya kawo wa shugaban hukumar INEC na wancan lokacin, Farfesa Attahiru Jega barazana, sa’ilin da ake tattara kuri’un zaben shugaban kasa.

Duk da abin da ya faru, Elder Godsday Orubebe ya zauna hankalinsa kwance tare da sauran manyan bakin da aka gayyata a dakin taron fadar shugaban kasa.

Sauran manyan kasar da su ka halarci bikin da aka yi sun hada da Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sanata, Ovie Omo-Agege.

Wata sabon gani: Dame Jonathan da Orubebe sun halarci bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari
Bikin kaddamar da littafin Aisha Buhari a Aso Villa
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Najeriya sun soki bikin kaddamar da littafin tarihin Aisha Buhari

Sarakuna irinsu Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar II, da Ooni na kasar Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi sun samu zuwa wajen wannan biki.

Haka zalika an hangi mai dakin tsohon mataimakin shugaban kasa, Hajiya Amina Namadi Sambo a Aso Villa, ita ce uwargidar Arch. Mohammed Namadi Sambo.

Dr. Kayode Fayemi, Simon Lalong, Atiku Bagudu, da Mai Mala Buni, sun wakilci Gwamnoni.

A jiyan kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yaba wa wargidar Shugaban kasar a taron, ya ce Aisha Buhari ba ta da tamka a tarihin Najeriya.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce mai dakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta banbanta da duka sauran Matan Shugabannin kasan da aka yi a baya a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel