JAMB ta bada sanarwa, an dakatar da rubuta jarrabawar UTME/DE na shekarar 2021

JAMB ta bada sanarwa, an dakatar da rubuta jarrabawar UTME/DE na shekarar 2021

- Joint Admissions and Matriculation Board ta fitar da muhimiyyar sanarwa

- An dakatar da rajistan jarrabawar UTME/DE da aka shirya za a fara a jiya

- Hukumar JAMB ta ce an samu tangarda ne ta bangaren aiki da lambar NIN

Hukumar Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) mai shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta dakatar da UTME.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an fasa gudanar da wannan jarrabawa kamar yadda aka tsara za a soma a ranar Alhamis, 8 ga watan Afrilu, 2021.

Shugaban harkar yada labarai da shirye-shirye na hukumar JAMB ta kasa, Dr. Fabian Benjamin, ya fitar da jawabi, inda ya bayyana wannan a jiyan nan.

KU KARANTA: JAMB ta soke cibiyoyin jarrabawa 22 a Najeriya

Fabian Benjamin ya ce an dakatar da zana jarrabawar ne domin a karkare ‘yan gyare-gyare da ake yi game da sha’anin lambobin sirrin da ake amfani da su.

Kamar yadda Dr. Benjamin ya bayyana, da zarar an kammala wannan, za a fara rubuta jarrabawar.

Jawabin ya ce:

“A da hukumar ta shirya cewa za a soma rajista ne a yau (8 ga watan Afrilu, 2021). Domin tabbatar da cewa an karkare duk wasu shirye-shirye kafin a soma aiki, hukumar ba ta buga talla ba, don ba a kammala aiki a kan tantance lambobin sirri na PIN da kuma aiki a kan manhajar da aka fito da shi domin masu jarrabawar UTME/DE 2021.”

JAMB ta bada sanarwa, an dakatar da rubuta jarrabawar UTME/DE na shekarar 2021
Masu rubuta jarrabawar UTME/DE
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Sabon littafin tarihin Aisha Buhari ya jawo mutane su na ta surutu

Jami’in hukumar ya ce an samu tangarda ne wajen hada lambar NIN da bayanan masu rubuta jarrabawar, a dalilin haka aka gagara fara rajistan a jiya.

“Jinkirin ya zo ne a dalilin wasu kalubale da ba mu hararo ba, da su ka bijiro mana wajen amfani da lambobin NIN. An shawo kan wannan matsala, kuma da zarar an kammala, za a soma shirin jarrabawar.”

Hukumar JAMB ta yi kira ga dalibai su yi hakuri. “Komai zai kankama, daga nan za a fito da talla domin masu zana jarrabawar su fara rajista.” Inji Benjamin.

Kwanakin baya aka ji cewa Hukumar JAMB mai shirya jarabawar neman gurbi a manyan makarantun gaba da sakandari, JAMB ta fito da sabon tsari.

JAMB ta yi kira ga 'yan Najeriya da suka zana jarabawar a shekarar bara da su duba sakamakon jarabawarsu ta hanyar amfani da layukan wayoyin salulansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel