Hukumar JAMB ta canza hanyar da ake bi domin duba sakamakon jarabawa

Hukumar JAMB ta canza hanyar da ake bi domin duba sakamakon jarabawa

Hukumar shirya jarabawar neman gurbi a manyan makarantun gaba da sakandari, JAMB ta yi kira ga yan Najeriya da suka zana jarabawar da su duba sakamakon jarabawarsu ta amfani da layukan wayoyin salulansu.

Idan za’a tuna a ranar Litinin ne JAMB ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar dalibai 312,000 da suka zana jarabawar a ranar Asabar, sai dai daliban da suka zana jarabawar a ranar Litinin sun gaza duba nasu sakamakon ta shafin yanar gizo.

KU KARANTA: Sanatoci sun nemi Buhari ya fito ya ma yan Najeriya jawabi game da Coronavirus

Hukumar JAMB ya canza hanyar da ake bi domin duba sakamakon jarabawa
Hukumar JAMB ya canza hanyar da ake bi domin duba sakamakon jarabawa
Asali: Depositphotos

Shugaban sashin watsa labaru na JAMB, Fabian Benjamin ya bayyana cewa hukumar ce ta rufe shafinta na yanar gizo a ranar Talata bayan wasu miyagu sun yi kokarin yin sauye sauye a sakamakon jarabawar dalibai.

“Mun saki sakamakon jarabawar dalibai 469,000 da suka zana jarabawar a ranar Litinin, don haka daliban zasu duba sakamakon jarabawarsu ne ta hanyar aikata Kalmar RESULT zuwa ga wannan lamba 55019 daga lambobin wayar da suka yi rajista dasu.

“Kada su duba sakamakon jarabawarsu ta yanar gizo saboda mun kulle shi bayan wasu miyagu sun yi kutse a shafin tare da kokarin sauya sakamakon jarabawar dalibai, tuni mun kaddamar da bincike a kan lamarin, kuma ba zamu fasa daukan matakin daya dace a kansu ba.” Inji shi.

Haka zalika jami’in ya yi tsokaci game da batun da ke yayatawa wai hukumar da gangan take tura dalibai nesa da garinsu don zana jarabawar, inda yace JAMB ba ta da hurumin tura dalibi wani wuri, don haka ba ta ke turawa ba.

“Dalibi ne da kansa yake zaban garin da yake son zana jarabawar, kuma da zarar cibiyoyin zana jarabawar dake garin sun cika sai mu dauke garin mu bar sauran garuruwan da suka rage.” Inji shi.

A wani labarin kuma, hukumar NYSC ta musanta rade radin da ake yayatawa ne cewa wai akwai wani dan bautan kasa daya kamu da cutar Coronavirus, inda ta ce babu gaskiya a cikin rade raden.

A ranar Laraba ne NYSC ta sanar da garkame dukkanin sansanonin horas da matasa masu yi ma kasa hidima dake fadin Najeriya tare da sallamar matasan daga sansanin.

Hukumar NYSC ta bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da suka gudanar a ranar Laraba, inda suka ce sun yanke shawarar kulle sansanonin horon yan bautan kasar ne saboda gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: