JAMB ta soke cibiyoyin jarrabawa 22 a fadin Najeriya, 1 kadai ke Arewa (Jerinsu)

JAMB ta soke cibiyoyin jarrabawa 22 a fadin Najeriya, 1 kadai ke Arewa (Jerinsu)

Hukumar shirya jarrabawan shiga makarantun gaba da sakandare watau JAMB ta sauke rijistan cibiyoyin zana jarrabawan yanar gizo 22 sakamakon cutan dalibai 11,823 kudi kimanin milyan 60.

Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana hakan a ganawar yanar gizon da yayi da wakilan wadannan cibiyoyi da abin ya shafa a ranar Alhamis.

Oloyede ya ce cibiyoyin sun zambaci daliban ta hanyar amsan kudi fiye da abinda aka tsara kan wasu sauye-sauye tare da yin satar hanyar samun OTP.

"Mun gayyato ku ganawar nan ne domin ji daga gareku tare da sanar da al'umma yadda wasu daga cikinku ke ayyukan zamba yayin yiwa dalibai rijista." Oloyede ya ce.

"Akwai wasu daga cikinku da suka cancanci a kirasu kwarrarun yan damfara."

"Wasunku sun karbi N3000 zuwa N5000 daga hannun dalibai kan abinda bai wuce N200 ba da sunan kudin aiki."

"Abinda kuka karba ya zarce milyan 59. JAMB na da isassahen hujja kan wannan damfarar saboda muna kallon kudaden da ake biyan cibiyoyin rijista domin ganin irin zamban da suke yi."

JAMB ta soke cibiyoyin jarrabawa 22 a fadin Najeriya, 1 kadai ke Arewa (Jerinsu)
JAMB ta soke cibiyoyin jarrabawa 22 a fadin Najeriya, 1 kadai ke Arewa (Jerinsu)
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari ya bada umurnin kada farashin wutan lantarki, amma ba zai shafi talaka ba - NERC

Cibiyoyin da abin ya shafa sune:

Jihar Abiya: Bright Stars, Aba (Dalibai 68); Flourish Computer Centre,

Jihar Akwa Ibom: Ibom-E-Library, Akwa Ibom-12; Chukwuemeka Odumegwu University, Igbariam.

Jihar Anambra: Deacons Digital Solutions Ltd. -96; Federal Poly, Oko 314, Mega Dataview, Onitsha-733.

Jihar Bayelsa: Linnet Paul Innovative Institute, Yenagoa- 3435; Niger Delta University-1200;

Jihar Edo: Diict, Benin-81; Gateway Edutech, Benin-10; Gifted Hands Science and Technology, Benin-223; NABTEB ICT Training Centre, Benin-291; Samuel Adegboyega University, Ogwa-670 da Supreme ICT Foundation, Benin-22.

Jihar Enugu: Elco ICT, Nsukka-538; Peaceland and Stalwart Solutions, Enugu-554; Union ICT-773;

Jihar Kaduna: Time online ICT, Sabon Tasha, Kaduna-67:

Jihar Lagos: Duntro High School, Surulere-21; Elite BusinessConsult, Ikorodu 218

Jihar Rivers: Ave Maria international academy, Rumuodara, Port Harcourt-1731.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng