2023: Takarar Bola Tinubu ta na samun karbuwa sannu a hankali a wajen Sarakan Yarbawa

2023: Takarar Bola Tinubu ta na samun karbuwa sannu a hankali a wajen Sarakan Yarbawa

- Kungiyar SWAGA ta na ta cigaba da kai wa Sarakunan yankin Kudu ziyara

- SWAGA ta na yi wa Bola Tinubu yakin neman Shugaban kasa a zaben 2023

- Wasu Sarakuna sun nuna goyon bayansu ga takarar Jigon APC, Bola Tinubu

Mai martaba Olu na kasar Ilaro, Sarkin Yewaland, Oba Kehinde Olugbenle da Mai martaba Sarkin Alake, Adedotun Gbadebo su na tare da Bola Tinubu a zaben 2023.

Jaridar Vanguard ta ce wadannan sarakuna sun nuna cewa su na goyon bayan takarar Asiwaju Bola Tinubu ne bayan kungiyar SWAGA 23 ta kai masu ziyara a jiya.

Sarakunan sun yi magana yayin da ‘yan kungiyar SWAGA 23 masu fafutukar ganin Bola Tinubu ya yi takarar kujerar shgaban kasa a babban zabe mai zuwa na 2023.

Bakin sarakunan ya hadu a kan cewa tsohon gwamnan na Legas ne ya fi dace wa da mulkin kasar. Oba Olugbenle, ya ce Yarbawa ba su da wanda ya fi Bola Tinubu.

KU KARANTA: Sauya-sheka: Gwamnan PDP ya watsawa Shugabannin APC kasa a idanu

Mai martaba Oba Olugbenle ya nuna cewa ya na tare da kungiyar SWAGA, ya ce jagoran na APC da su ke mara wa baya, ya taimaka wajen cigaban kasar nan.

“Tarihin da ya bari bayan ya yi mulkin jihar Legas ya tabbatar da cewa babu shakka shi ne wanda ya fi dace wa da wannan aiki (shugaban kasa)", inji Oba Olugbenle.

“Ba maganar jam’iyya ba ce, ana batun wanda za a kawo ne. Shi ne ‘dan takarar da ya fi dace wa kowace jam’iyya ta tsaida daga Kudu, cigaban kasa ake magana.”

Alake na kasar Egbaland, Sarki Gbadebo ya yi magana makamaciyar ta takwaransa, ya ce kungiyar magoya bayan jagoran na jam’iyyar APC za ta kai labari.

2023: Takarar Bola Tinubu ta na samun karbuwa sannu a hankali a wajen Sarakan Yarbawa
Bola Tinubu wajen rajistar APC Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kici-kacan kusoshin APC ya jawo an kama Sanata Okorocha

Mai martaba Oba Gbadebo, ya ce tun ba yau ba, shi ya hango cewa Bola Tinubu ya rike Najeriya.

A jiya kun ji kungiyar South West Agenda 23 ta dage da yi wa Asiwaju Bola Tinubu fafutuka. Sanata Dayo Adeyeye yake jagorantar wannan tafiya ta Bola Tinubu.

A makon jiya Dayo Adeyeye, ya jagoranci tawaga zuwa fadar Sarkin Remoland, Babatunde Ajayi.

Wadanda ke yi wa Dayo Adeyeye rakiya sun hada da Bosun Oladele, Rotimi Makinde, Arch Dunni Opayemi, Suraj Adekunbi Ishola sai kuma Abiodun Ishiaq Akinlade.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng