Ta leko ta koma: Mu ba mu ce za mu goyi-bayan Bola Tinubu a 2023 ba inji Afenifere

Ta leko ta koma: Mu ba mu ce za mu goyi-bayan Bola Tinubu a 2023 ba inji Afenifere

- Kungiyar Afenifere ta musanya cewa tana goyon-bayan takarar Bola Tinubu

- Sola Lawal ya fitar da jawabi a jiya, ya na yi wa kungiyar SWAGA martani

- Lawal ya ce Afenifere ta na makokin mutuwar Yinka Odumakin ne yanzu

Kungiyar da ke kare hakkin mutanen Kudu maso yammacin Najeriya, Afenifere, ta musanya zargin yi wa Bola Tinubu mubaya’a game da zaben 2023.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Talata, Afenifere ta bayyana cewa ba ta fito ta nuna goyon baya ga Bola Tinubu ko wani ‘dan takara ba.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kungiyar SWAGA, Sanata Prince Dayo Adeyeye, ya fada wa Duniya cewa sun samu goyon bayan Pa Reuben Fasoranti.

KU KARANTA: Mulki ka ke nema – Magoya bayan Atiku sun fadawa Malami

Afenifere ta fitar da jawabi ne ta bakin Darektan yada labarai, Sola Lawal, inda ta ce babu wani ‘dan takarar shugaban kasa a 2023 da ta ba goyon-bayan ta.

Sola Lawal yake cewa har yanzu kungiyar Afenifere ta na makokin mutuwar Yinka Odumakin ne, wanda a dalilin haka ta dakatar da duk wasu ayyuka da ta ke yi.

Lawal ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a kyale Pa Fasoranti mai shekara 96 a Duniya ya huta bayan ya sauka daga kujerarsa ta shugaban Afenifere kwanaki.

A watan jiya ne Reuben Fasoranti ya ajiye mukaminsa bayan ya yi shekaru 12 ya na jagorantar kungiyar. Dattijon ya mika ragamar Afenifere ga Cif Ayo Adebanjo.

KU KARANTA: 2023: Gwamnonin APC da za su iya marawa Bola Tinubu baya

Ta leko ta koma: Ba mu ce za mu goyi-bayan Bola Tinubu a 2023 ba inji Afenifere
Shugabannin Afenifere a fadar Aso Villa
Asali: UGC

Darektan na Afenifere ya ce babu yadda Reuben Fasoranti zai yi magana a madadin kungiyar Afenifere tun da ya riga ya yi murabus makonni uku da su ka wuce.

“Yadda Adeyeye ya ke kutsawa cikin da’irar Afenifere a lokacin da ake makokin rashin da aka yi, rashin girmamawa ne da rashin tausayi, kuma babu dalilin hakan.”

Afenifere ta yi kira ga tsohon jigonta, Sanata Adeyeye ya shiga sahun masu makoki a wannan lokaci.

Kafin yanzu kun ji cewa tsohon shugaban Afenifere, Reuben Fasoranti, ya ce babban jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya cancanci ya zama shugaban kasa a 2023.

Reuben Fasoranti ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da kungiyar the South-West Agenda for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa ke Akure, a jihar Ondo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel