Ramadan: Za mu daina hulda da duk wani ‘Dan sari da ya kara kudin kaya inji BUA

Ramadan: Za mu daina hulda da duk wani ‘Dan sari da ya kara kudin kaya inji BUA

- Kamfanin BUA zai hukunta wadanda su ka tada farashin kaya a Ramadan

- Shugaban kamfanin BUA ya ce yin hakan zai jawo a karbe lasisin ‘yan sari

- Abdulsamad Isyaku Rabiu ya bada tabbacin farashin kaya ba za su tashi ba

Yayin da musulmai a fadin Duniya su ke shirin maraba da watan Ramadan, kamfanin BUA ta ja-kunnen ‘yan kasuwa game da tada farashin kaya.

Shugaban kamfanin BUA Group, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya gargadi abokan huldarsu da cewa su guji yin sama da farashin kaya a watan azumi.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta bayyana, Abdulsamad Isyaku Rabiu ya ce kamfaninsu zai hukunta wanda aka samu ya na tada farashin kaya.

KU KARANTA: Dangote bai son ana takara da shi a kasuwa - BUA

Hukuncin da kamfanin BUA zai dauka shi ne janye lasisin kasuwanci daga hannun duk wani ‘dan kasuwa da ke tsauwala wa Bayin Allah cikin azumi.

Har ila yau, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu ya bada tabbacin cewa BUA ba zai kara farashi a Ramadan da kuma bayan wannan wata mai alfarma ba.

Shugaban kamfanin ya bayyana wannan ne ta bakin babban jami’in da ke lura da kasuwancinsu a yankin arewacin Najeriya, Alhaji Mohammad Adakawa.

Mohammad Adakawa yake cewa BUA sun tanadi isassun kayan da za a bukata a wannan lokaci da abubuwa su ke wahala saboda karin farashi da ake yi.

KU KARANTA: Bankin Duniya zai agazawa Gwamnatin Najeriya wajen yaki da talauci

Ramadan: Za mu daina hulda da duk wani ‘Dan sari da ya kara kudin kaya inji BUA
Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu Hoto: www.infoguideafrica.com
Asali: UGC

Ya ce: “Ina tabbatar maku da cewa kayan da mu ke da su a ajiye za su gamsar da duka jihohin Arewa. Mu na da ton-ton na sukari a Sharada da za a bukata a Kano, Kebbi, Jigawa, Yobe, Maiduguri, Zamfara, Katsina da duka sauran jihohin Arewa.”

Adakawa ya ce abin da yake jawo tashin farashi da azumi shi ne karancin fetur a dalilin canjin farashin dala da kuma haraji, ya ce a bana kaya ba za su tashi ba.

Ku na da labari cewa a jerin Attajiran Duniya da mujallar Forbes ta fitar a 2020, 'Yan Najeriya hudu ne kacal su ka samu shiga, daga ciki akwai Abdul Samad Rabiu.

A ‘yan shekarun bayan nan, shugaban kamfanin na BUA ya ribanya arzikinsa, mujallar Forbes ta na yi masa hasashen ya na da kusan fam Dala biliyan 4.6.

Asali: Legit.ng

Online view pixel