Jigon PDP ya zargi Gwamna Tambuwal da kokarin tsokano rikici saboda harin takara a 2023
- Ana shirin gudanar da zaben Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa maso yamma
- Wani jigon jam’iyya, Adamu Musa Lere, ya zargi Gwamnan Sokoto da kawo sabani
- Adamu Musa Lere ya ce Aminu Tambuwal na neman saba yarjejeniyar da aka tsara
Wani babba a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Alhaji Adamu Musa Lere, ya na zargin gwamna Aminu Waziri Tambuwal da jawo rigimar cikin-gida.
Adamu Musa Lere ya fito ya na jifan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, da laifin kawo sabani a PDP saboda burinsa na takara a zaben 2023.
A wani jawabi da ya aika wa jaridar Solacebase, jigon jam’iyyar adawar ya bayyana cewa Waziri Tambuwal ya na raba kan jam’iyya a Arewa maso yamma.
KU KARANTA: Manyan PDP sun dura Zamfara, sun zauna da Matawalle a kan komawa APC
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar PDP na reshen Arewa maso gabas wanda za a gudanar a garin Kaduna.
A cewar Adamu Musa Lere, an tsaida magana cewa za a ba jihar Kano wasu muhimman kujeru, amma daga baya gwamna Tambuwal ya saba wa yarjejeniyar.
Daga cikin kujerun da aka ba jihar Kano akwai mataimakin shugaban jam’iyya da shugaban mata na reshen Arewa maso yamma, da kuma Ex-officio national.
“Sai kawai aka ji gwamnan Sokoto wanda ba ya wajen taron, ya saya wa wani jigon PDP a jihar Kano fam na neman kujerar mataimakin shugaban jam’iyya.”
KU KARANTA: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a Kano a 2023 - Kwankwaso
“An yi hakan ne da nufin raba kan ‘ya ‘yan jam’iyya a Arewa maso yamma.” Inji Adamu Lere.
Lere ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar PDP su kashe wutar wannan rigima da ta ke neman kunno kai saboda gudun abin da ya faru a 2019 ya maimaita kansa.
Har ila yau, jigon adawar ya ba uwar jam’iyya shawarar cewa ka da ta yi wasa da zuciyar siyasar Najeriya watau jihar Kano, domin a nan ne ake da tulin kuri’u.
Kwanakin baya kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bada gudumuwar kayan abinci ga mutanen Arewa da ke jihar Oyo.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bada wannan gudumuwa ne a sakamakon rikicin Shasha da aka yi, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuwa da dukiyar al'umma.
Asali: Legit.ng