Kungiya ta yi wa Ministan Buhari raddi na kokarin hana Atiku tsayawa takara a zaben 2023

Kungiya ta yi wa Ministan Buhari raddi na kokarin hana Atiku tsayawa takara a zaben 2023

- Amalgamated Atiku Support Group ta soki Ministan shari’an Najeriya

- Kungiyar ta yi raddi bayan AGF ya kai karar Atiku Abubakar gaban kotu

- Wannan kungiya ta ce Abubakar Malami ba zai yi nasara a shari’ar ba

Wata kungiya da ake kira Amalgamated Atiku Support Group ta ce Minista shari’a, Abubakar Malami SAN ya na harin kujerar shugaban kasa ne.

Kamar yadda The Cable ta rahoto, Amalgamated Atiku Support Group ta ce Ministan ya na gani zai sha kunya domin ba zai kai ga cinma burinsa ba.

Kungiyar ta yi wannan bayani ne a matsayin martani bayan babban lauyan gwamnatin ya shigar da kara, ya na neman a hana Atiku Abubakar takara.

KU KARANTA: An karrama Goodluck Jonathan a jihar Bauchi, ya samu sarauta

Darektan yada labarai na wannan kungiya, Remi Adebayo, ta ce an dade da raba gardama game da salsalar tsohon mataimakin shugaban Najeriyar.

Amalgamated Atiku Support Group ta ke cewa abin dariya ne a tafi kotu har yanzu ana kalubalantar Atiku da cewa shi ba ‘dan Najeriya ba ne.

Remi Adebayo ta ke cewa hakar da Ministan yake yi ba za ta taba cin ma ruwa a gaban Alkali ba.

Ta ce: “Idan za a tuna, an daldale maganar kalubalantar asalin Atiku Abubakar a babban kotun daukaka kara, a karshe kotun koli ta tabbatar da hukuncin.”

Kungiya ta yi wa Ministan Buhari raddi na kokarin hana Atiku tsayawa takara a zaben 2023
AGF ya ce Atiku Abubakar ba 'Dan Najeriya ba ne
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Gwamnonin Jihohin APC da ake ganin za su yi wa Bola Tinubu halacci

“An yi wannan shari’a ne wajen sauraron karar korafin zaben shugaban kasa” inji Remi Adebayo.

“Aikin da Malami yake yi ya nuna burinsa na neman dare wa kujerar shugaban kasa bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a shekarar 2023.” Inji ta.

“Yunwarsa za ta fito a yadda ya murje ‘yan jam’iyyarsa da ke harin takara, yanzu ya koma kan Atiku wanda yake gani shi ne babban kalubale a gabansa.”

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya bada labarin yadda wasu Mukarrabansa su ka kaurace masa saboda ya fadi zabe a 2015.

Goodluck Jonathan ya ce a lokacin da yake ofis, ba sai ya san mutum sannan ya ke ba shi mukami ba, ya ce alfarma ce ta ke kashe kasa ta hana a cigaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel