'Ƴan Kwakwazo' ba su isa hana Buhari cigaba da fita ƙasasahen waje ba, Hadimar Shugaban Kasa

'Ƴan Kwakwazo' ba su isa hana Buhari cigaba da fita ƙasasahen waje ba, Hadimar Shugaban Kasa

- Lauretta Onochie, hadiman Shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da martani ga masu kokawa kan tafiyarsa zuwa Landan ganin likita

- Onochie ta ce hayaniya da kwakwazo ba zai taba hana Buhari dena zuwa duba lafiyarsa wurin likitocinsa da ya saba zuwa tsawon shekaru 40 ba

- Jagoran masu zanga-zangar Revelution Now, Omoyele Sowore ya yi alkawarin zai jagoranci wasu yan Nigeria su tafi masaukin Buhari su cigaba da zanga-zangar neman ya koma Nigeria

Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie, ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da ikon ya fita kasashen waje domin ganin likitocinsa kuma babu wanda ya isa hana shi.

Ta yi wannan martanin ne bayan maganganun da aka rika yi bayan shugaban kasar ya tafi Landan domin duba lafiyarsa, a shafinta na Twitter.

'Ƴan Kwakwazo' ba su isa su hana Buhari cigaba da fita kasasahen waje ba, Hadimar Shugaban Kasa
'Ƴan Kwakwazo' ba su isa su hana Buhari cigaba da fita kasasahen waje ba, Hadimar Shugaban Kasa. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Hakan ya janyo zanga-zanga a masaukin Buhari da ke Landan wato Abuja House.

Jagoran zanga-zangar Revolution Now, Omoyele Sowore, ya shirya yin sabon zanga-zanga a yau Laraba da nufin tilastawa Buhari komawa Nigeria inda likitoci suka shiga yajin aiki.

A martaninta, Onochie ta bayyana cewa babu wani irin hayaniya da zata hana Buhari tafiya duba lafiyarsa a kasashen waje kamar yadda ya saba tsawon shekaru.

Ta wallafa a Twitter, "Shekara mai zuwa, Shugaban kasa @MBuhari zai tafi a duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

"Muna nan tun 2016. Hayaniyar dai da aka saba ne. Don haka martanin ba zai canja ba.

"Akalla sau daya a shekara, mutane a duniya sukan tafi su ga likitansu musamman wanda suka saba gani tsawon shekaru 40.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bi dare sun sace shugaban kwamitin riƙo jam'iyyar APC a gidansa

"@MBuhari ba zai yi watsi da likitansa da ya saba gani tsawon shekaru 40 ba saboda masu hayaniya su ji dadi. Wannan mugun nufi ne kuma Buhari baya kula masu mugun nufi."

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel