Hawaye sun kwaranya a jihar Kaduna yayinda gwamnati ta sallami ma'aikata

Hawaye sun kwaranya a jihar Kaduna yayinda gwamnati ta sallami ma'aikata

- Gwamnatin Nasir El-Rufa'i ta sallami ma'aikatan kananan hukumomi a Kaduna

- Yayinda wasu ke jimamin haka, wasu sun ce Allah ya zaba musu mafi alkhairi

- Gwamnatin jihar ta ce tayi hakan ne don tsaftace aikin gwamnati

Hawaye sun kwaranya a sakatariyar karamar hukumar Jema'a dake Kafanchan, jihar Kaduna ranar Laraba yayinda gwamnatin jihar ta mika wasikun sallama ga wasu ma'aikata 82.

Wannan sabon kora ya biyo bayan jita-jitan da aka kwashe makonni ana ji cewa gwamnatin jihar na shirin rage ma'aikata a kananan hukumomin 23.

Yayinda kamfanin dillancin labarai NAN ta ziyarci Sakatariyar, an ga ma'aikatan rike da takardunsu cikin takaici da bakin ciki.

A cewar wasikar, an yi hakan ne a yunkurin da akeyi na kawo gyara da sauyi kananan hukumomin jihar.

DUBA NAN: Kwamishinan Yan sandan Lagos ya ɗauki ƙwaƙkwaran Mataki don gujema abinda ya faru a Owerri

Hawaye sun kwaranya a jihar Kaduna yayinda gwamnati ta sallami ma'aikata 82
Hawaye sun kwaranya a jihar Kaduna yayinda gwamnati ta sallami ma'aikata 82 Credit: @GovKaduna
Source: Facebook

KU KARANTA: Ta tabbata: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai

Daya daga cikin ma'aikatan da abin ya shafa wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa ta wani dalilin gwamnatin za ta dauki irin wannan mataki a lokaci irin yanzu da mutane ke fama.

"Ta wani dalili gwamnati za ta yi irin wannan abu yanzu. Shin basu san ana cikin halin kunci bane a kasar nan." yace.

"Da kyar mutane ke rayuwa da dan albashin da suke samu, sannan kuma sai kawai a kwace musu abinci."

Wani ma'aikacin wanda shima ya bukaci a sakaye sunansa saboda gudun kada a hanashi fansho ya bayyanawa NAN cewa ya rungumi kaddara.

A bangare guda, Daya daga cikin daliban makarantar FCFM dake Afaka, jihar Kaduna ya yi bayani kan ainihin yadda suka samu kubuta daga hannun yan bindiga.

Daya daga cikin daliban, Francis Paul, ya bayyana cewa yan bindigan ne suka sakesu da kansu.

Hukumar Sojin Najeriya ta saki sunayen daliban su biyar.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel