Labari da duminsa: Jerry Gana Ya Koma PDP, Ya Ce 'Babu Gwamnati a Nigeria'

Labari da duminsa: Jerry Gana Ya Koma PDP, Ya Ce 'Babu Gwamnati a Nigeria'

- Farfesa Jerry Gana, tsohon ministan labarai ya fita daga jam'iyyar SDP ya koma PDP

- A jawabinsa wurin bikin komawa jam'iyyar PDP, Jerry Gana ya ce babu gwamnati a Nigeria

- Har wa yau, tsohon ministan ya kuma ce ƙasar ta doshi nutsewa hakan yasa ya zama dole PDP ta karbi mulki ta ceto kasar

Tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana, ya yi ikirarin cewa babu gwamnati a Nigeria kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gana ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke koma jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, tare da magoya bayansa masu yawa a ranar Laraba.

A watan Maris ɗin 2018, Gana, mamba na kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, ya fice ya koma jam'iyyar SDP.

KU KARANTA: An cafke hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a Jallo a Nasarawa

Labari da duminsa: Jerry Gana Ya Koma PDP, Ya Ce 'Babu Gwamnati a Nigeria'
Labari da duminsa: Jerry Gana Ya Koma PDP, Ya Ce 'Babu Gwamnati a Nigeria'. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi a Bida, Jihar Niger, wurin bikin tarbarsa, Gana ya ce kasar na nutsewa kuma tana bukatar taimakon gaggawa.

Farfesa Gana, "Yau ba ranar yin lakca bane. Ba ranar kamfen bane. Muna son muyi murnar cewa mun dawo mun haɗe wuri guda; kuma za muyi aiki tare yadda ya kamata sannan muyi yaƙin neman zaɓe gadan-gadan.

"Akwai gwamanti a jihar Niger? Domin mutane da yawa ba su sani ba, ko a tsakiya? A matakin tarayya, ba mu da gwamnati."

Tunda farko, shugabannin jam'iyyar daga mazaɓu uku sun bawa magoya bayan PDP tabbacin cewa sun shirya karɓe jihar Niger su ceto jihar daga hannun APC da ta lalata al'amura.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a asibitin Aso Rock

A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya ya ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164