An cafke hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a Jallo a Nasarawa

An cafke hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a Jallo a Nasarawa

- Hukumar NDLEA ta ce kama wani hatsabibin dilalin miyagun kwayoyi, Sami Ashoko, a jihar Nasarawa

- Femi Babafemi, kakakin hukumar ya ce an yi nasarar kama Ashoko ne da taimakon bayannan sirri

- Babafemi ya ce jami'an hukumar sun kai sumame gidan da Ashoko ke ajiye miyagun kwayoyi sun kwato buhunan ganyen wiwi 100

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama dilalin miyagun kwayoyin da ake nema ruwa a jallo a jihar Nasarawa, Sami Ashoko, kuma ta kai samame wurin ajiyar kayansa makil da miyagun kwayoyi inda aka kama buhuna 10 na da nauyinsa ya kai 1.095.3 kg, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, a ranar Talata ya ce dubun wasu masu safarar miyagun kwayoyi ta cika inda aka kama su a Iyamho, karamar hukumar Etsako ta jihar Edo da haramtattun kayansu mai dauyin 1,330kg da ake niyyar kai wa jihar Bauchi.

An cafke hatsabibin dilalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a Jallo a Nasarawa
An cafke hatsabibin dilalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a Jallo a Nasarawa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

A cewarsa, an kama dukkanin su biyun ne a ranar Juma'a a yayin da suke kokarin rarrabar da haramtattun kayan nasu domin cin kasuwar bikin Easter.

"A Nasarawa, an kama Ashoko, mai shekaru 39, dan asalin garin Ibilo a Akoko Edo ta jihar Edo a garin Shinge, Lafia bayan samun bayannan sirri game da shi.

"Tawagar yan sanda sun kai sumame wurin ajiyarsa a Lafia sun gano buhuhunan ganyen wiwi 100 da nauyinsu ya kai tan 1.1 ko 1095.3 kg," a cewar Babafemi.

A cewar kwamandan NDLEA na jihar Nasarawa, MrJustice Arinze, "Sam Ashoko hatsabibin dilalin miyagun kwayoyi ne da muka dade muna nema ruwa a jallo a jihar Nasarawa."

"Ya yi niyyar sayar da kayan da aka sace ne cikin makonni biyu yayin bikin Easter."

KU KARANTA: Abin da yasa Buhari bai bar tsohon IGP Adamu ya ƙarasa ƙarin wata 3 da ya masa ba, Ministan Ƴan Sanda

Ya ce hukumar bata taba yin kamu mai girman wannan ba tun kafa ta a shekarar 1999.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel