Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a asibitin Aso Rock

Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a asibitin Aso Rock

- Allah ya yi wa, Sa'idu Afaka, direban shugaban kasa Muhammadu Buhari rasuwa

- Afaka ya rasu ne a ranar Talata a asibitin Aso Rock a Abuja bayan ya dade yana jinya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Afaka da gwamnatin jihar Kaduna

Fadar shugaban kasa, a ranar Talata, ta sanar da rasuwar Master Warrant Officer, Sai'idu Afaka, direban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Afaka ya rasu ne a asibitin fadar shugaban kasa a ranar Talata bayan ya dade yana fama da rashin lafiya kamar yadda kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar.

Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a Aso Rock
Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a Aso Rock
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Shehu ya ce Shugaba Buhari yana yi wa gwamnati da mutanen jihar Kaduna ta'ziyyar marigayi Afaka da ya ce mutum ne mai gaskiya, kwararre wanda ya rike aikinsa da kyau yayin rayuwarsa..

Shugaba Buhari ya tuna a 2016 lokacin da Afaka ya tsinci jaka makil da kudaden kasashen waje yayin aikin hajji a Saudiyya ya kuma mika wa jami'an hukumar aikin hajji wadda hakan yasa gwamnatin Saudiyya ta yaba masa.

KU KARANTA: An cafke hatsabibin dilalin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a Jallo a Nasarawa

Shugaban kasar ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya saka masa da gidan aljanna tare da addu'ar Allah ya bawa iyalansa da abokai hakurin jure rashinsa.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel