Da duminsa: Allah yayi wa wani dan majalisar wakilan tarayya rasuwa

Da duminsa: Allah yayi wa wani dan majalisar wakilan tarayya rasuwa

- Allah yayi wa dan majalisar tarayya, Suleiman Aliyu rasuwa

- Ya rasu yana da shekaru 53 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya

- Kafin rasuwarsa, shi ke wakiltar mazabar Lere a majalisar wakilai ta tarayya

Kwanaki kadan bayan rasuwar dan majalisar tarayya, Haruna Maitala, wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Lere ta tarayya a jihar Kaduna, Suleiman Aliyu, ya rasu yana da shekaru 53 a duniya.

Aliyu ya rasu a yau Talata da rana a asibitin koyarwa na Barau Dikko dake jihar Kaduna bayan gajeriyar rashin lafiya.

Cikin kwanakin nan ne dan majalisar yayi nasara a kotun daukaka kara inda aka jaddada shi a matsayin dan takara kuma wanda yayi nasara a zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 na mazabar Lere a tarayya.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun sheƙe ƴan Boko Haram 12 yayin da suka kai hari sansaninsu a Borno

Da duminsa: Allah yayi wa wani dan majalisar wakilan tarayya rasuwa
Da duminsa: Allah yayi wa wani dan majalisar wakilan tarayya rasuwa. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara

A wata shari’a mai cike da tarihi da aka yanke a ranar Juma’a, 2 ga watan Nuwamban 2020, kotun ta soke wani hukunci wanda aka yanke.

Kotun, wacce Alkalai Obietonbara Daniel-Kalio, Saidu Tanko Hussaini da Olutodun Adepope-Okojie, sun yanke hukuncin cewa hukuncin ba zai yuwu a kotu ta gaba ba sakamakon dogaro da sashi na 287, sakin layi na biyu na kundun tsarin mulkin kasar Najeriya na 1999.

A wani labari na daban, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuntar zamani wanda aka ga wasu matasan jihar Kogi dauke da bulalai suna tsabga wa wasu matasa biyu da suke zanga-zangar nuna kiyayya ga Shugaba Muhammadu Buhari.

A bidiyon wanda Premium times ta wallafa a ranar Litinin, 5 ga watan Afirilu an ga matasan suna cire 'Buhari Must Go' daga jikin bango ana basgarsu da bulalai a mazaunansu.

Sun umarci matasan da su sake yin fenti a bango yayin da suke shan ruwan bulalai.

Alamu sun nuna cewa har yanzu matasan jihar Kogi suna goyawa Shugaba Buhari baya. A cikin bidiyon, an ji wani matashi da yake dukan masu zanga-zangar yana cewa 'jihar Kogi ta Buhari ce'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng