2023: Gwamnonin APC 6 da za su iya marawa Bola Tinubu baya ya zama Shugaban kasa

2023: Gwamnonin APC 6 da za su iya marawa Bola Tinubu baya ya zama Shugaban kasa

Bisa dukkan alamu, Asiwaju Bola Tinubu zai nemi takarar shugaban kasa a APC. Gwamnoni suna da matukar karfi a siyasa, kuma su na da ta-cewa a jam’iyya.

Mun kawo wasu gwamnoni da ake ganin za su iya marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023.

1. Babajide Sanwo-Olu

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya na tare da Bola Tinubu 100-bisa-100. Zai yi duk abin da zai iya domin ganin Tinubu ya samu tikitin APC idan har ya tsaya takara.

2. Gboyega Oyetola

Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola zai goyi-bayan Bola Tinubu wanda ake zargin ‘danuwansa ne, kuma shi ya yi ruwa da tsaki wajen ganin gwamnan ya dare kan mulki a zaben 2018.

3. Dapo Abiodun

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya na cikin ‘yan a-mutun Asiwaju Bola Tinubu a jam’iyyar APC. Zai mara masa baya a 2023 domin ya maida alherin da Jigon ya yi masa a 2019.

KU KARANTA: Matasan Arewa sun yi kaca-kaca da Tinubu

4. Babagana U. Zulum

Wani gwamna da ake ganin zai ba takarar Bola Tinubu goyon-baya shi ne Farfesa Babagana Umara Zulum. Gwamnan ya na cikin masu goyon-bayan mulki ya koma Kudu a 2023.

5. Aminu Bello Masari

Akwai yiwuwar gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya goyi bayan Bola Tinubu ya samu tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

6. Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na tare da Bola Tinubu. Gwamnan bai taba boye tarayyarsa da jagoran na APC ba, kuma da alamu ya shirya taimaka masa a zaben 2023.

KU KARANTA: Ina Jam’iyyar ANPP, Jonathan ya fito da ni a siyasa - Bala Mohammed

2023: Gwamnonin APC 6 da za su iya marawa Bola Tinubu baya ya zama Shugaban kasa
Wasu Gwamnonin APC da Bola Tinubu Hoto: legit.ng
Asali: Facebook

Akwai sauran gwamnonin da ake ganin za su iya ba Bola Tinubu goyon-baya, daga ciki akwai Abdullahi Sule da Mai Mala Buni da su ke mulkin jihohin Nasarawa da kuma Yobe.

A jiya ne aka ji cewa tsohon shugaban kungiyar nan ta Afenifere, Reuben Fasoranti, ya ce jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya cancanci ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa Reuben Fasoranti ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da kungiyar South-West Agenda for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a garin Akure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng