An saka sunan Goodluck Jonathan a titin Bauchi, an kuma nada shi sarauta
- Gwamantin jihar Bauchi ta karrama tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta saka sunansa a wani titi
- A ranar Talata ne Goodluck Jonathan ya sanar cewa Gwamnan Bauchi ya saka wa sabon titin Ƙaura zuwa Mira sunansa
- Jonathan ya kuma yi wa masarautar Bauchi godiya bisa naɗa shi sarautar Jigon Bauchi yayin ziyarar da ya kai jihar
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya ma wani titi sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Suleiman Adamu da mambobin majalisar masarautar Bauchi sun kuma bawa Jonathan sarauta yayin ziyarar da ya kai Jihar.
Jonathan ya sanar da hakan a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook a ranar Talata.
DUBA WANNAN: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda
Ya bayyana gamsuwarsa da irin ayyukan da Gwamna Bala Mohammed ya yi inda ya ce ayyuka ne da za su amfani al'umma.
Jonathan ya wallafa cewa: "Ina godiya ga gwamnatin jihar Bauchi da mutanen jihar saboda sanya suna na a sabon titin Ƙaura zuwa Miri.
"A yau, ina tarayya da gwamnan Bauchi Sanata Bala Mohammed da sauran ƴaƴan jihar wurin kaddamar da babban titin Goodluck Jonathan Bye Pass.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a asibitin Aso Rock
"Na yi farin cikin ganin cewa gwamnan yana aiwatar da ayyuka da za su amfani al'umma da nufin inganta rayuwarsu.
"Ina godiya ga Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Suleiman Adamu da mambobin majalisar masarautar Bauchi bisa tarba ta karamci da naɗa ni sarautar Jigon Bauchi yayin ziyarar."
A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.
Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.
Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.
Asali: Legit.ng