Forbes ta saki jerin masu kudin nahiyar Afrika, akwai yan Najeriya 4, 2 Kanawa ne (Kalli Jerin)
Hamshakin mai kudin Najeriya kuma Bakano, shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ne mutum mafi arziki a nahiyar Afrika a shekarar 2020. Rahoton Forbes.
Wannan shine karo na tara a jere da attajirin ya zarcewa dukkan masu halin nahiyar.
Jerin masu kudin ya mayar da hankali kan kasashen Afrika takwas masu kudi; yayinda kasar Masar da Afrika ta kudu suka da masu kudi biyar-biyar a jerin, Najeriya na da hudu, sannan kasar Maroko mai biyu.
Rahoton ya bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya zo na daya da arzikin dala bilyan goma ($10.1 billion) na kasuwancinsa a Siminti, man fetur, flawa, Timatur da Sukari, sai Nassef Sawiris na kasar Masar mai arziki dala bilyan takwas ($8 billion) ya zo na biyu, sai Mike Adenuga mai kamfanin sadarwan Glo ya zo na uku.
Yan Najeriyan da suka shiga jerin masu kudin nahiyar sabanin Dangote sune Abdus Samad Isyaka Rabiu, Mike Adenuga, da Folorunsho Alakija.
Ga jerin masu kudin nan:
Aliko Dangote $10.1 billion
Nassef Sawiris $8 billion
Mike Adenuga $7.7 billion
Nicky Oppenheimer $7.7 billion
Johann Rupert $6.5 billion
Issad Rebrab $4.4 billion
Mohamed Mansour $3.3 billion
Abdulsamad Rabiu $3.1 billion
Naguib Sawiris $3 billion
Patrice Motsepe $2.6 billion
Koos Bekker – $2.5 billion
Yasseen Mansour – $2.3 billion
Isabel dos Santos – $2.2 billion
Youssef Mansour – $1.9 billion
Aziz Akhannouch – $1.7 billion
Mohammed Dewji – $1.6 billion
Othman Benjelloun – $1.4 billion
Michiel Le Roux – $1.3 billion
Strive Masiyiwa – $1.1 billion
Folorunsho Alakija – $1 billion
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng