Kubi Sahun mu ku shiga yajin aiki ko mu ciku tarar 5 Miliyan, NARD ta gargaɗi Likitocin COVID19
- Ƙungiyar likitoci NARD ta yi barazanar zata ci tarar duk wani likita da yaƙi yin biyayya wajen shiga yajin aikin da ƙungiyar ta fara ranar 1 ga watan Afrilu
- Ƙungiyar ta tura saƙo ga dukkan mambobinta inda ta bayyana musu duk wanda ya yi kunnen uwar shegu da hukuncinta to zai biya miliyan N5m
- Haka kuma ƙungiyar tace zata dakatar da duk wanda yaƙi yin biyayya daga riƙe kowanne irin muƙami a ciki ƙungiyar na tsawon shekara biyu
Ƙungiyar Likitocin ƙasar nan NARD ta umarci likitocin dake cibiyar kula da waɗanda suka kamu da cutar COVID19 da subi sahu, suma su tsunduma yajin aiki.
KARANTA ANAN: Wani Mutumi ya kashe ɗan shekara 57 saboda zargin yana da ɓoyayyar Alaƙa da Matarsa
NARD ta yi iƙirarin cewa idan har suka ƙi bin umarnin ƙungiya to za'a ci tarar su na kuɗi kimanin miliyan N5m, jaridar PM News ta ruwaito.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa duk reshen da yaƙi yiwa uwar ƙungiyar biyayya wajen shiga yajin aikin da suka fara ran ɗaya ga watan Afrilu, to bazai samu damar riƙe wani muƙami a ƙungiyar ba na tsawon shekaru biyu.
Barazanar da ƙungiyar ta yi na cin tarar miliyan N5m ga duk wani reshe da yaƙi bin umarnin uwar ƙungiyar na ƙunshe ne a wani saƙo da ta tura ma mambobin ƙungiyar.
A saƙon da ƙungiyar ta tura ta ce:
"Hukuncin duk wata cibiya da ta yi kunnen uwar shegu da yajin aikin da ake yi shine biyan tarar kuɗi miliyan N5m, da kuma dakatarwa daga rike wani muƙami a ƙungiyar na tsawon shekaru biyu."
KARANTA ANAN: Ba zamu iya biyanku Cikakken Albashin Watan Maris ba, Ganduje ya faɗawa ma'aikata
A kwanakin baya NARD ta bayyana shiga yajin aikin sai baba ta gani a ranar 1 ga watan Afrilu bisa abinda suka bayyana da cewa gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan su albashin su, da kuma wasu haƙƙoƙin su.
Sai dai gwamnatin ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen hana likitocin shiga yajin aikin a ranar 31 ga watan Maris, amma hakan bai samu ba, inda ƙungiyar likitocin suka yi fatali da yarjejeniyar da suka yi da gwamnatin.
A wani labarin kuma Atiku ya na fuskantar danyen kalubale game da zaben 2023 daga Gwamnatin Buhari
Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce dokar kasa ba ta ba Atiku Abubakar damar neman shugaban kasa ba.
Abubakar Malami ya ce a lokacin da aka haifi Atiku, inda aka haifi Atiku wato Jada ba ta cikin Najeriya.
Asali: Legit.ng