Babban kamu: Jami’an kwastam sun tare tabar wiwin Naira Biliyan 1 a Najeriya

Babban kamu: Jami’an kwastam sun tare tabar wiwin Naira Biliyan 1 a Najeriya

- Jami’an Kwastam sun cafke tabar wiwi na kusan Naira Biliyan 1 a Legas

- Ma’aikatan kwastam sun tare buhunan ganyen wiwi ne ta iyakokin ruwa

- Wannan ya na cikin gagaruman nasarar da hukumar kwastam su ka samu

A ranar Jum’a, 2 ga watan Afrilu, 2021, hukumar kwastam ta yi nasarar kama ton shida na ganyen da ake zargin cewa tabar wiwi ne

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto kimanin kilogram 6, 000 na wiwi aka yi ram da su a Legas.

Adadin tabar wiwin da aka kama sun kai buhuna 120 masu cin kilo 50. Ana lissafin darajar wiwin da aka kama ya kai Naira biliyan daya.

KU KARANTA: Hukuma ta taso Sarkin Kano, Aminu Bayero da laifin cin kudin filaye

Rahotannin sun bayyana cewa jami’an bangaren Western Marine Command na Legas ne su ka cafke wadannan kaya da aka shigo da su.

An tare kayan ne a bayan ruwan garin Legas. A tarihin kwastam, wannan ne kame na biyu da ya fi kowane girma da aka yi a Najeriya.

Shugaban bangaren iyakokin gabashin Najeriya, Mista Peters Olugboyega, ya ce wannan na cikin gagaruman nasarorin da su ka taba samu.

Babban kamu: Jami’an kwastam sun tare tabar wiwin Naira Biliyan 1 a Najeriya
Tabar wiwi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojoji sun yi gaba da wasu jiragen saman da mu ka ba su - Wike

Ku na da labari cewa a ranar 2 ga watan Afrilu, 2021, aka rantsar da Mohammed Bazoum a matsayin sabon shugaban Jamhuriyyar Nijar.

An haifi sabon shugaban kasa Mohammed Bazoum ne a ranar farko a Junairun shekarar 1960. Hakan ya na nufin ya na da shekara 61 a Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng