'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna

- Wasu mahara da ake zargin yan bindiga ne sun halaka mutum 5 a karamar hukumar Chikun a Kaduna

- Wadanda aka kashe sune Samson Danladi, Luka Gajere, Amos Ali, Titus Baba da Damali Musa

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Mr Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar

Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Katarma da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna inda suka halaka mutane biyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mr Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce a ranar Lahadi maharan sun raunata mutum daya.

'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe mutane 5 a sabuwar harin da suka kai a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

A cewarsa, mutum dayan da ya jikkata yana nan yana samun kulawan likitoci a wata jiha da ke makwabtaka da Kaduna.

KU KARANTA: Yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta laƙume gidansu a Suleja

Duk da kwamishinan bai fada lokacin da aka kai harin ba, ya bayyana wadanda suka rasu kamar haka Samson Danladi, Luka Gajere, Amos Ali, Titus Baba da Damali Musa.

"A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an tsaro karkashin Operation Safe Haven, sun ruwaito cewa an yi fada tsakanin matasa a kauyen Atuku da ke karamar hukumar Jema'a. Yayin fadar, wasu matasa biyu sun kaiwa wani Afiniki Thomas hari sun masa rauni mai muni a goshinsa.

"An kama daya daga cikin maharan Sani Safiyanu domin bincike. An garzaya da wanda aka yi wa raunin zuwa asibiti don yi masa magani.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ɓarawo Ya Maƙale a Cikin Ramin Da Ya Haƙa Don Shiga Coci Ya Yi Sata

"Kazalika, Dakarun na Safe Haven yayin sintiri sun tsinci gawar wani Paul Simon, mazaunin kauyen Yagbak a karamar hukumar Zangon Kataf. An bada sanarwar bacewar mammacin a ranar 24 ga watan Maris, 2021. An birne gawarsa," sanarwar ta kara da cewa.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel