Mukarrabin Jonathan da wasu sun bi Shugaba Buhari har Landan, sun yi masa zanga-zanga

Mukarrabin Jonathan da wasu sun bi Shugaba Buhari har Landan, sun yi masa zanga-zanga

- Mutanen Najeriya sun yi zanga-zanga a gidan da Buhari yake zaune a Landan

- Reno Omokri ne ya jagoranci muutane zuwa gidan da ake sauke shugaban kasa

- Omokri ya zargi Buhari da sakacin gyara harkar kiwon lafiya da ilmi a Najeriya

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omokri, da wasu ‘yan Najeriya sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Najeriya da ke birnin Landan, Ingila.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa Reno Omokri sun yi zanga-zangar ne a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya je ganin likita a kasar.

Reno Omokri da ‘yan tawagarsa sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda Muhammadu Buhari ya bar gida, amma ya zo kasar wajen domin duba lafiyarsa.

KU KARANTA: Ingila za ta ba Najeriya gudumuwar maganin rashin tsaro

Masu zangar-zangar sun fito dauke da kati masu kunshe da sakonnin da su ke aika wa a gaban gidan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke zaune.

Tsohon mai ba Goodluck Jonathan shawara ya soki yadda shugaban Najeriyar ya zo wurin likitocin Landan a lokacin da bai gina asibiti a gida ba.

“Ya bar Najeriya a ranar da likitoci su ka fara yajin-aikinsu.” Reno Omokri ya fada a wurin.

Ya ce: “Ba ya gina wa mutanensa asibitoci, amma ya na zuwa nan ya huta da kyau a kasar da ake bin doka da oda. Me zai hana ya yi irin haka a kasarsa?”

KU KARANTA: Hadimar Mai dakin Shugaban kasa ta rubuta littafi a kan Aisha Buhari

Mukarrabin Jonathan da wasu sun bi Shugaba Buhari har Landan, sun yi masa zanga-zanga
Shugaba Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

“Duka yaransa a Ingilar nan su ka yi karatu. Bai gina wa ‘yan Najeriya ko da makaranta daya ba. Idan ba su da lafiya, dukkansu nan su ke zuwa.” Inji sa.

Omokri ya koka a kan matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwan da ake fama da shi a Najeriya saboda halin da gwamnatin Buhari ta jefa al’ummar kasar.

Dazu kun ji cewa kasar Amurka ta zargi mahukuntan Najeriya da laifin mahaukaciyar sata da hana mutane damar fadar abin da su ke so a shekarar 2020.

Jam’iyyar adawa ta PDP da wasu kungiyoyi sun gamsu da wannan rahoto da Amurka ta fitar, su ka ce kama-karyar da ake yi, ta zarce na lokacin Sani Abacha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel