Yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta laƙume gidansu a Suleja

Yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta laƙume gidansu a Suleja

- Allah ya yi wa wasu yara biyu rasuwa a Anguwar Dawaki da ke Suleja, Jihar Niger

- Hakan ya faru ne sakamakon gobara da ta tashi a gidansu a daren ranar Alhamis

- Alhassan Jibirin Yanji, mahaifin yaran ya yi kokarin ceto su amma hakan bai yi wu ba

Yara biyu, Suraiya mai shekaru 7 da Habib mai shekaru 9 sun kone sakamakon wata gobara da ta kona wani babban gida a Anguwar Dawaki a garin Suleja da ke jihar Niger.

Daily Trust ta ruwaito cewa mahaifin yaran, Alhaji Jibrin Yanji, wanda ya samu rauni garin kokarin ceto yaran yana karban magani a asibiti da ke Suleja.

Yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta lakume gidansu a Suleja
Yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta lakume gidansu a Suleja. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram Sunyi Kisa a Borno, Sun Sace Kayan Abinci da Dabobi

Wani mazaunin garin, Bashir Ibrahim, ya ce gobarar ta faru ne a daren ranar Alhamis misalin karfe 3 a lokacin da wuta ta kama a dakunan da wadanda abin ya shafa suke ciki.

Ya ce yaran suna kwance a dakinsu yayin da mahaifinsu yana dakinsa, a lokacin da ya farka sai ya lura hayaki ya turnuke gidan baki daya.

Ya ce, "Abin mamaki babu wutar lantarki a dukkan unguwar ta Dawaki a lokacin da gobarar ta tashi don haka babu wanda ya san sanadin gobarar."

KU KARANTA: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

Daga bisani an yi wa yaran jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci a safiyar Juma'a.

Ya bayyana cewa babu wani abin amfani da aka ciro daga gidan domin mahaifiyar yaran ma bata gida a lokacin da abin ya faru.

Shugaban karamar hukumar Suleja, Alhaji Abdullahi Maje, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce ana bincike domin gano sanadin gobarar.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel