Bidiyon Boko Haram farfaganda ne, ba su suka harbo jirgin Soji ba: Binciken Masana

Bidiyon Boko Haram farfaganda ne, ba su suka harbo jirgin Soji ba: Binciken Masana

- Yan ta'adda Boko Haram sun dauki alhakin hadarin da jirgin yakin Soji yayi

- Amma hukumar Sojin sama NAF ta ce karya ne hada tayi

- Hukumar NAF ta ce Sojojinta biyu ke tukin jirgin lokacin da ta bace a sararin samaniya

Wani masanin tsaro a kasar Sweden, Hugo Kaaman, ya ce bidiyon da Boko Haram ke ikirarin ta harbo jirgin Sojoji tsohuwar bidiyon abinda ya faru a kasar Syriya ne a 2012.

Jirgin yakin Sojin Najeriya NAF 475 da aka turo leken asirin kan yan Boko Haram ta bace da yammacin Laraba a jihar Borno.

A ranar Alhamis, hukumar NAF tace da yiwuwa jirgin ya samu hadari ne.

Amma ranar Juma'a, yan ta'addan Boko Haram sun saki bidiyon da ke ikirarin cewa su suka harbo jirgin daga sararin samaniya.

Tsokaci kan bidiyon, Hugo Kaaman ya ce bidiyon da Boko Haram ta saki a kasar Syriya ya faru a 2012.

"Boko Haram ta saki bidiyon dake nuna cewa ta harbo jirgin yakin NAF. Dubi cikin bidiyon, da alamun tun a sama ya kama da wuta. Amma wannan ba gaskiya bane," Kaaman yace.

"Boko Haram ta yi amfani wani bidiyon daga 2012 dake nuna yadda jirgi mai saukar angulu SyAAF ta fado a garin Idlib."

"Da gaske jirgin ya fadi, amma babu hujjan baro jirgin akayi ko kuma wani abu ya lalace."

KU DUBA: Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna

KU DUBA: Gobara ta kama babbar kasuwar kayan mota a garin Ibadan

Hukumar Sojin saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa jirgin yakinta Alpha Jet (NAF475) da ta bace a sararin samaniya ta yi hadari.

Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da safiyar Juma'a. 2 ga Afrilu, 2021.

Gabkwet ya bayyana cewa akwai matuka biyu cikin jirgin kuma ya bayyana sunayensu matsayin, FL John Abolarinwa da FL Ebiakpo Chapele.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng