Da duminsa: Gobara ta kama babbar kasuwar kayan mota a garin Ibadan

Da duminsa: Gobara ta kama babbar kasuwar kayan mota a garin Ibadan

Hawaye sun kwaranya yayinda gobara taci shahrarriyar kasuwar kayayyakin mota ta Araromi dake Agodi-Gate, Ibadan, babbar birnin jihar Oyo ranar Asabar.

Yan kasuwa sun kira jami'an kwana-kwanan jihar yayinda wasu ke kokarin kashe wutar.

Amma rashin isasshen ruwa ya zama matsala yayinda wuta ta cigaba da ci bal-bal.

Yayinda jami'an kwana-kwana suka isa wajen, sun gaza kusantan wajen saboda zafin wuta. Daga nesa suke kokarin kashe wutar.

Duk kokarin da akayi na kashe wutar ya ci tura.

Har da Masallacin da ke kasuwar bai tsira ba.

Wannan sabon gobara ya shiga jerin gobaran da akayi kasuwanni daban-daban a Najeriya.

KU KARANTA: Yajin aikin Likitoci: Sabon jariri ya mutu a asibiti sakamakon rashin Likita

DUBA NAN: Bidiyon Boko Haram farfaganda ne, ba su suka harbo jirgin Soji ba: Binciken Masana

A jiya, rahotanni sun nuna cewa mumunar gobara ta ci babbar kasuwar garin Funtua, dake jihar Katsina.

Gobarar ta ci kasuwar ne misalin karfe biyu na daren Juma'a, 2 ga watan Afrilu, 2021.

Hakazalika irin wannan gobara ya faru a kasuwar jihar Yobe da kuma kasuwar jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel