Yanzu-yanzu: Yan bindiga suk bindige shugabannin Miyetti Allah har lahira a Nasarawa

Yanzu-yanzu: Yan bindiga suk bindige shugabannin Miyetti Allah har lahira a Nasarawa

- Yan bindiga sun kai mumunan hari kan shugaban Miyetti Allah a Nasarawa

- Wannan shine karo na farko da za'a kaiwa jagoran kungiyar Fulani Makiyaya hari

- Gwamnan jihar ya kira ga jama'a kada suyi tayar da hankulansu

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun hallaka shugaban kungiyar Fulani Makiyaya Miyetti Allah na jihar Nasarawa, Alhaji Mohammed Musa.

An kashe Hussaini tare da shugaban kungiyar na karamar hukumar Toto, Muhammad Umar, da daren Juma'a a jihar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Nasarawa, Ramham Nansel, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki, rahoton Daily Trust.

"A ranar 2/4/2021 misalin karfe 7 na yamma, an samu labarin wasu yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kashe Mohammed Hussaini, shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Nasarawa, da kuma Mohammed Umar, shugaban kungiyar Miyetti Allah na karamar hukumar Toto, a kasuwar Garaku," yace.

"Bayan samun labarin, kwamishanan yan sandan CP Bola Longe, ya tura jami'an Operation Puff Adder II wajen inda aka dauki gawawwakinsu kuma aka kai asibiti."

DUBA NAN: Yajin aikin Likitoci: Sabon jariri ya mutu a asibiti sakamakon rashin Likita

Yanzu-yanzu: Yan bindiga suk bindige shugabannin Miyetti Allah har lahira a Nasarawa
Yanzu-yanzu: Yan bindiga suk bindige shugabannin Miyetti Allah har lahira a Nasarawa
Asali: Original

KU KARANTA: Bidiyon Boko Haram farfaganda ne, ba su suka harbo jirgin Soji ba: Binciken Masana

Mun kawo muku cewa Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace a harin da ƴan bindiga suka kai masa, sai da suka yi ta musayar wuta da ƴan sanda na tsawon mintuna 15.

Kun ji bayanin yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa Soludo farmaki a wani dakin taro dake Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba.

Wasu ƴan sanda guda 3 da suke kula da lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin, sannan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng