Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero

Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai Ilorin komen gida ne, saboda nan ne dangin mahaifiyarsa.

Alhaji Aminu Ado Bayero jika ne ga sarki na takwas na Ilorin, Alhaji Abdulkadir Dan Bawa, wanda yayi rayuwa daga 1919 zuwa 1959. Dan uwa ne na dangi ga sarkin yanzu, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari.

Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero
Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

A yayin jawabinsa da yayin ziyarar gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq, Aminu Ado Bayero ya ce ya je tushensa ne don neman albarka daga dangin mahaifiyarsa.

Sarkin ya yi amfani da damar wuri ta'aziyyar mahaifin Gwamnan jihar. Ya yi fatan rahamar Allah ga marigayin.

Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero
Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda wani mutum ya riƙa kuka yana birgima cikin taɓo don budurwarsa ta ƙi yarda ta aure shi

"Makasudin zuwa na shine dawowa gida, inda tushena yake. A gareni, Kano da Ilorin duk dayane. Nan ne dangin mahaifiyata kuma ina matukar farin cikin zama a cikinsu.

"Ba wannan bane karo na farko ko na biyu da na zo ba. Amma wannan zuwan na musamman ne saboda na hau karagar magabatanmu. Ina godiya ga Allah," in ji Sarki Aminu.

Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero
Hotuna: Dalilan kai ziyara ga Ilorin - Sarki Aminu Bayero. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Ya cigaba da cewa "Na zo neman albarka daga dangin mahaifiyata da shugabanni wadanda na sakankance sun taka rawar gani wurin bada gudumawa a rayuwarta."

A bangaren Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce masarautun gargajiya na taka rawar gani wurin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya ga al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: