Da duminsa: Dan majalisar wakilai ya mutu a hadarin mota
- Najeriya ta sake rashin babban dan majalisar tarayya
- Wannan shine dan majalisa na 10 da zai mutu a ofis tun rantsar da su a 2019
- Hanarabul Maitala ya mutu tare da 'dansa da mutanen da tare da shi
Wani dan majalisar wakilan tarayya, Haruna Maitala ya rigamu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota ranar Juma'a a hanyar Bade-Gitata yayinda ya nufi zuwa Jos.
A cewar Premium Times, dan majalisan ya samu hadarin ne tare da 'dansa, direbansa, da dogarinsa kuma dukkansu sun mutu.
Kafin mutuwarsa, Maitaka yana wakiltan mazabar Jos ta Arewa da Bassa a majalisar wakilan tarayya.
Mutuwarsa na zuwa ne kimanin wata daya bayan mutuwar, Yuguda Killa, daga jihar Jigawa.
Maitala ne dan majalisa na uku da ya mutu wannan shekara.
Daga 2019 zuwa yanzu, yan majalisun tarayya 10 suka mutu.
KU DUBA: Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna
KU KARANTA: Bidiyon Boko Haram farfaganda ne, ba su suka harbo jirgin Soji ba: Binciken Masana
A wani labarin kuwa, Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace a harin da ƴan bindiga suka kai masa, sai da suka yi ta musayar wuta da ƴan sanda na tsawon mintuna 15.
Mun kawo muku yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa Soludo farmaki a wani dakin taro dake Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba.
Wasu ƴan sanda guda 3 da suke kula da lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin, sannan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne.
Asali: Legit.ng