Boko Haram: Kasar Ingila za ta taimakawa Najeriya wajen kawo karshen matsalar tsaro
- Birtaniya za ta taimaka wajen samar da zaman lafiya a Najeriya da Afrika
- Ministan sojin Ingila, James Heappey, ya bayyana haka da ya kawo ziyara
- Najeriya da Birtaniya sun dade su na da kyakkyawar dangantaka mai karfi
Kasar Birtaniya ta bayyana niyyar ta na aiki da Najeriya domin a kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake ta faman fuskanta a kasar nan.
Jaridar This Day ta rahoto karamin Ministan sojojin na Birtaniya, James Heappey, ya na wannan bayani a lokacin da ya kawo ziyara zuwa Najeriya.
“Najeriya abokiyar aiki ce mai muhimmanci ga Birtaniya. Kasashen nan na mu biyu su na fuskantar kalubale daga masu tsaurin addini irinsu Boko Haram, zuwa masu laifuffuka a zirin Guinea.”
KU KARANTA: Sarkin Gombe ya yabi alakar Shugaba Buhari da Farfesa Osinbajo
“Birtaniya a shirya ta ke ta yi aiki da abokanmu na Najeriya, domin a magance wadannan barazanar tsaro da ake fuskanta, a wanzar da zaman lafiya a yammacin Afrika."
A jawabin da Jakadan Birtaniya a Najeriya ya yi, ya ce zuwan Ministan har kasar nan ya nuna muhimmancin alakar da ke tsakanin kasar Ingia da Najeriya.
“Birtaniya ta na da tsohon tarihin alaka ta tsaro da yankin yammacin Afrika da kuma dangantaka da dakarun Najeriya da rundunar hadin-gwiwa da ke yakin Boko Haram.’”
Mista James Heappey ya zauna da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari; Ministan tsaro Janar Bashir Magashi (rtd) da gwamnan Borno, Babagana Zulum.
KU KARANTA: Amurka ta fitar da mummunan rahoto a kan Najeriya a 2020
Ministan kasar wajen ya samu damar zama da hafsoshin sojojin Najeriya; Rear Admital Awwal Zubairu Gambo; Janar Lucky Irabor.
James Heappey ya bayyana muhimmancin a kare hakkin Bil Adama wajen yakin da ake yi.
Dazu kun ji labari cewa ana maidawa juna martani tsakanin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Rundunar Sojin sama a kan wasu jiragen yaki.
Gwamna Nyesom Wike ya na zargin sojojin sama da karkatar da jiragen da su ka samu ta hannun gwamnatinsa, ya ce an maida jiragen Arewa maso gabas.
Asali: Legit.ng