Jam’iyyar PDP ta samu abin magana bayan Amurka ta bankado jerin ta’adin Gwamnatin APC

Jam’iyyar PDP ta samu abin magana bayan Amurka ta bankado jerin ta’adin Gwamnatin APC

- Kasar Amurka ta fitar da rahoto maras dadi game da Gwamnatin Najeriya

- Amurka na zargin Gwamnatin APC da sata, zalunci, tauye hakkin al'umma

- Jam’iyyar adawa ta PDP da wasu kungiyoyi sun gamsu da wannan rahoto

Jaridar Punch ta ce kasar Amurka ta zargi mahukuntan Najeriya da laifin mahaukaciyar sata da hana mutane damar fadar abin da su ke so a shekarar 2020.

Amurka ta bayyana wannan ne a wani rahoto da ta fitar game da Najeriya a ranar Talatar nan, mai taken ‘2020 Country Reports on Human Rights Practices.’

Daga cikin laifuffukan da kasar ta Amurka ta ambata a wannan rahoto, akwai yadda aka kama tsohon shugaban hukumar EFCC na Najeriya, Ibrahim Magu.

KU KARANTA: Buhari: Ka da mu bari masu mugun nufi su raba kan Najeriya

Amurka ta ce ana tafka sata da sauran laifuffuka a kowane matakin gwamnati, ba tare da an yi amfani da dokokin da za su hukunta masu wannan aikin ba.

Bayan zargin sata, rahoton ya ce gwamnatin Najeriya ta na tauye hakkin ‘yan jarida, tare da hana ayi magana kan ta’adin da ake yi kamar sata da magudin zabe.

Bayan fitowar wannan rahoto, jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi maza, ta fito ta yi magana, ta na mai Allah-wadai da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar PDP ta amince da rahoton da Amurka ta fitar. Kola Ologbondiyan, ya ce al’ummar kasar sun san da irin zalunci da kama-karyar da ake yi a mulkin APC.

KU KARANTA: Sarkin Gombe ya yabi alakar Shugaba Buhari da mataimakinsa

Jam’iyyar PDP ta samu abin magana bayan Amurka ta bankado jerin ta’adin Gwamnatin APC
Shugaban Najeriya Buhari

Sakataren yada labaran na PDP yake cewa tauya hakkin mutane da ake yi a yau, ya zarce abin da aka fuskanta a lokacin da Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya.

Haka zalika tsohon shugaban kwamitin kare hakkin Bil Adama, Malachy Ugwumadu, ya soki gwamnati.

Shugaban kungiyar Coalition in Defence of Nigerian Democracy and Constitution, Ariyo-Dare Atoye, ya ce rahoton da aka fitar ya fallasa irin ta’asar da ake yi.

A lokacin da ake kukan ba a kama masu laifi, sai aka ji cewa wata babban kotu a jihar Sokoto ta yankewa wani mai damfara hukuncin daurin shekaru 70 a kurkuku.

EFCC ta shigar da karar Hamzat Muhammad Bashar ne tun Nuwamban 2019 a kan zargin laifuffuka 12 da su ka hada da damfara, yaudara, da zamba cikin aminci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel