Da duminsa: Jirgin yaƙi na sojin saman Najeriya dake taimakon sojin kasa a arewa, ya ɓace
- Jirgin sojin saman Najeriya ya bace a yankin arewacin Najeriya
- Kakakin rundunar sojin kasa, Air Commodore Edward Gabkwet, ya sanar da hakan
- Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar ana kokarin gano inda jirgin saman yake
Jirgin yaki na sojin saman Najeriya dake ayyukan yau da kullum a yankin arewacin Najeriya ya bace.
Wannan yana kunshe ne a wata wallafa da kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkweet yayi a shafinsa na Twitter kuma Legit.ng ta gani a daren Laraba, 31 ga watan Maris.
Ya wallafa: "Wani jirgin NAF dake ayyukan yau da kullum na taimakawa dakarun sojin kasa a yankin arewacin Najeriya ya bace. Ana kokarin ganin an gano inda yake. Karin bayani na nan tafe."
KU KARANTA: Shugaban CCT ya suburbudi maigadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'
KU KARANTA: Matar Aure Tayi wa Ɗan Kishiya Mugun Duka, ya Sheƙa Lahira
Karin bayani na nan tafe...
A wani labari na daban, Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce kasar nan na fuskantar zaman lafiya duk da irin kalubelen tsaro da take ciki.
Rundunar sojin kasar nan sun kasance suna yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas sama da shekaru 10.
The Cable ta ruwaito cewa, dakarun suna cigaba da gwagwarmaya da 'yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasar nan.
Asali: Legit.ng