‘Yan fashi sun yi wa ‘Yan Sanda shelar zuwa, kuma sun fasa bankuna da rana sun saci miliyoyi

‘Yan fashi sun yi wa ‘Yan Sanda shelar zuwa, kuma sun fasa bankuna da rana sun saci miliyoyi

- ‘Yan fashi da makami sun shiga jihar Delta, sun kai hari a wasu bankuna biyu

- Wadannan miyagu sun yi gaba da makudan kudi ba tare da an iya kama su ba

- Sai da ‘Yan fashin su ka sanar da ‘Yan Sanda cewa su na nan, za su kawo hari

A ranar Talata, 30 ga watan Maris, 2021, ‘yan fashi da makami su ka auka wa bankuna biyu a garin Issele-Uku, karamar hukumar Aniocha, jihar Delta.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa wadannan ‘yan fashi sun shiga wani gidan mai da wurin cin abinci, su ka yi barna a lokacin da su ka yi wannan ta’adi.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan fashin sun yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a Issele-Uku, sannan sun yi awon-gaba da miliyoyin kudi daga bankuna.

KU KARANTA: Barayi sun balle wani ofishi a Majalisar Tarayya

Sai da wadannan ‘yan fashi su ka sanar da ‘yan sanda shirin su na kawo hari a ranar Litinin, kuma a karshe dai su ka samu nasarar yin abin da su ka so.

A lokaci guda ‘yan fashin su ka auka wa wasu bankuna biyu, su ka saci kudi da motoci, sannan kuma wasu su ka tare gidan mai da wani wurin cin abinci.

Wani mazaunin karamar hukumar Aniocha ya ce haka wadannan miyagu su ka yi kusan sa’a guda su na aika-aika da rana-tsaka, ba tare da an yi komai ba.

Wasu ‘yan fashin su shiga cikin bankunan su ka rutsa mutanen ciki, yayin da ragowar su ka fito waje, su ka rika yin ruwan harsashi a kan sauran mutanen gari.

‘Yan fashi sun yi wa ‘Yan Sanda shelar zuwa, kuma sun fasa bankuna da rana sun saci miliyoyi
Gwamnan Delta, Sanata Ifeanyi Okowa
Asali: UGC

KU KARANTA: Ka da a taba filayen Mahaifinsu Saraki, sai an karkare shari’a - Kotu

A cewar wani mutumin garin Ogbeofu, daga cikin wadanda aka kashe har da wani ‘dan kasuwa.

Da aka tuntubi jami’an tsaro, kakakin ‘yan sanda na jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai iya bada wani cikakken bayani ba.

Kwanakin baya wasu barayi da aka kama a kasuwar Alaba a Legas, sun bayyana cewa shugabannin kasuwar su ke biyan su, su shiga shaguna su yi sata.

Wasu mutane biyu da ake zargin su da wannan laifi na fashi da makami sun ce 'yan kasuwan ne su ke amfani dasu a matsayin 'yan daba a cikin wannan kasuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng