2023: Gwamnan APC ya na goyon-bayan mulkin Najeriya ya koma Kudu bayan Buhari

2023: Gwamnan APC ya na goyon-bayan mulkin Najeriya ya koma Kudu bayan Buhari

- Gwamnan jihar Nasarawa ya na cikin masu goyon baya mulki ya bar Arewa

- Abdullahi Sule ya ce abin da ya dace shi ne kujerar shugaban kasa ta rika yawo

- Sule ya na kuma so ‘Yan Arewa maso tsakiya su samu shugabancin jam’iyya

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna cewa ya na goyon-bayan a rika zagaya wa da mulkin Najeriya tsakanin bangarorin kasar nan.

Mai girma gwamna Abdulllahi Sule ya ce akwai bukatar shugaban kasan da za ayi ya fito daga kudu.

Jaridar The Nation ta ce Abdulllahi Sule ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zauna da Magoya-bayan Sanata Umaru Tanko Al-Makura a Lafia.

KU KARANTA: Modu Sheriff ya ziyarci Gwamna Sule a kan harin Shugabancin APC

Umaru Tanko Al-Makura ya na cikin wadanda su ke neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa a zaben da za ayi a tsakiyar shekarar nan.

Magoya bayan Sanata Al Makura sun zabi gwamnan Nasarawa Sule a matsayin jagoran wannan tafiya, domin ganin tsohon gwamnan ya yi nasara.

Gwamnan yake cewa ba a adalci ba ne Arewa ta samu mulki ta hanyar, sannan kuma daga baya ace ba za ayi goyin bayan ‘Yan kudu su rike kasar ba.

Sule ya na ganin Arewa maso tsakiya ya dace da kujerar shugaban APC saboda sauran yankunan Arewa su na da shugaban kasa da shugaban majalisa.

2023: Gwamnan APC ya na goyon-bayan mulkin Najeriya ya koma Kudu bayan Buhari
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jami'an Gwamnati ke yaudarar Buhari - Shugaban Majalisa

Ya ce: “Shiyasa ban taba cewa komai game da kiran da ake yi na kai kujerar shugaban kasa zuwa Kudu ba. Saboda ba na tunanin akwai matsala da hakan.”

Gwamna Sule ya nanata batun adalci, ya ce idan za a kai kujerar shugaban kasa zuwa Kudu, to ya kamata ne shugaban APC ya fito daga Arewacin Najeriya.

Ku na da labari cewa akwai gwamnonin Arewa da ke da wannan ra’ayi, daga cikinsu akwai Babagana Umara Zulum, Nasir El-Rufai da Abdullahi Ganduje.

Gwaman Aminu Bello Masari (Katsina) ya na cikin wadanda su ke ganin ya kamata mulki ya bar Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel