Tsohon Shugaban PDP ya dawo ya na neman kujerar Shugaban Jam’iyyar APC
- Ali Modu Sheriff zai nemi takarar shugaban jam’iyyar APC na kasa
- Tsohon gwamnan ya nemi Gwamnan Nasarawa ya mara masa baya
- Abdullahi Sule ya na goyon bayan a kai takarar Arewa maso tsakiya
Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya nuna sha’awar fito wa takarar shugaban jam’iyyar APC na kasa a zaben da za ayi a shekarar bana.
Jaridar The Nation ta ce Sanata Ali Modu Sheriff ya bayyana wannan ne a ranar Laraba, a lokacin da ya gana da gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Sule.
Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, Ali Modu Sheriff ya kai ziyara zuwa gidan gwamnan jihar Nasarawa da ke garin Lafia ne domin ya samu goyon-baya.
KU KARANTA: ‘Dan Obasanjo ya daurewa Gwamna Bello gindi ya nemi mulki
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ali Sheriff ya zauna da gwamna Abdullahi Sule, inda ya nemi ya mara masa baya a zaben da za ayi a watan Yuni.
Sanata Sheriff ya bayyana cewa zai shiga wannan takarar ne idan har za a kai kujerar shugaban jam’iyyar na kasa zuwa yankin Arewa maso gabas da ya fito.
Ganin yadda ya rike kujerar Sanata da gwamna na tsawon shekara takwas, kuma ya shugabanci jam’iyyar PDP, Sheriff ya na da duk abin da APC ta ke bukata.
Sanata Sheriff ya shaida wa gwamna Sule cewa ya san ya na kokarin ganin an kai takarar zuwa yankinsa na Arewa maso tsakiya, musamman jihar Nasarawa.
KU KARANTA: An nemi a kara wa'adin rajistar 'Ya 'yan jam'iyyar APC
Tsohon gwamnan ya ce zai mara wa Arewa ta tsakiya baya muddin APC ta bar masu kujerar.
Mai girma Abdullahi Sule ya yaba wa jagoran na APC, ya nuna masa ba ya tare da shi, ya kuma bukaci ya mara masu baya su fito da sabon shugaban APC na kasa.
A jawabinsa, Sanata Sheriff ya yaba da irin kokarin da gwamna Sule yake yi wajen gyara Nasarawa.
Dazu kun ji cewa Gwamna Yahaya Bello ya ce duk abin da ake yi, sai dai Bola Tinubu ya goyi-bayan wani matashi ya fito takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC.
Ganin yadda ake ta rade-radi game da zaben 2023, Alhaji Yahaya Bello ya bayyana cewa Bola Tinubu ya san iyakarsa, ba zai fito neman kujerar Shugaban kasa ba.
Asali: Legit.ng