Tsaro: Yadda barayi suka balle ofishi a majalisar tarayya

Tsaro: Yadda barayi suka balle ofishi a majalisar tarayya

- Barayi sun balle tare da shiga wani ofishi a ginin majalisar dattawan Najeriya da ke Abuja

- Kai tsaye 'yan daban suka shiga ofishin Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar wakilai

- Dan majalisar ya bukaci jami'an tsaro da su yi bincike tare da gano wadanda suka yi mugun aikin

Wasu wadanda ake zargin 'yan daba ne sun balle tare da shiga ofishin dan majalisar wakilai, Benjamin Kalu.

Lamarin ya tada hankalin jama'a don ya bayyana gazawa a tsaron ginin majalisar tarayyar kasar nan.

Ofishin na nan a lamba 1.53 na majalisar wakilan Najeriya da ke ginin majalisar tarayya da ke Three Arms Zone, Abuja.

Baya ga dakarun sojin da ke tsaron ginin majalisar, akwai sama da jami'an tsaro 300 da suka hada da 'yan sanda, jami'an NSCDC, jami'an FRSC da kuma na tsaron farin kaya da ke ginin majalisar.

Duk da haka, rashin tsaro, fashi da makami, sata, balle ofisoshi da sauran laifuka sun ci gaba da faruwa a ginin majalisar.

Ba sau daya ba ko sau biyu ba, ana samun satar motoci, batiran motoci da kuma sata a shagunan da ke farfajiyar ginin majalisar.

A yayin bayyana yadda aka balle ofishinsa, Kalu ya ce hadimansa sun rufe kofofin ofishinsa a ranar Talata, 5 ga watan Mayu, bayan zaman majalisar na karshe.

Tsaro: Yadda barayi suka balle ofishi a majalisar dattawa
Tsaro: Yadda barayi suka balle ofishi a majalisar dattawa. Hoto daga Kalu Media Team
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa

"Bayan dawowa ta ofishina a safiyar Talata, 12 ga watan Mayu, daya daga cikin hadimai na ya gano cewa dukkan wutar ofishina an kashe ta.

"Bayan mun bincika, mun yi matukar girgiza ganin cewa hanyar da za ta sada mu da ofishina a bude, don ta ita ake iya shiga wurin.

"Mun gano cewa an kawar da shingen katakon da ake amfani da shi wajen rufe hanyar shiga ofishin. An watsar da kaya masu tarin yawa da ke cikin ma'adanarsu, alamu da ke nuna an balle tare da shiga," yace.

Kalu, wanda ya fitar da hoto da bidiyon yadda aka balle masa ofishinsa, ya jaddada cewa an kulle ofishinsa tsaf a ranar Talata da ta gabata kuma babu wanda ya bari ya shiga har sai yau da safe.

Dan majalisar ya ce a halin yanzu ana duba takardun ofishinsa don gano abubuwan da aka kwashe.

Ya yi kira ga jami'an tsaro da su yi bincike sosai don gano abinda ya faru a ofishinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel