Shugabannin kasuwa ne suke biyanmu mu fasa shagunan abokanan sana'arsu muyi musu sata - Cewar wasu barayi

Shugabannin kasuwa ne suke biyanmu mu fasa shagunan abokanan sana'arsu muyi musu sata - Cewar wasu barayi

Wasu barayi da aka kama a kasuwar Alaba dake jihar Legas, sun bayyana cewa shugabannin kasuwar ne suke biyan su kudi duk wata suna shiga shagunan mutane suna yi musu sata

Wasu mutane biyu da ake zargin su da fashi da makami da jami'an tsaro suka kama a jihar Legas da laifin fasa shagunan mutane a kasuwar Alaba dake Ojo, sun bayyana cewa wasu 'yan kasuwa ne ke amfani dasu a matsayin 'yan daba a cikin kasuwar.

'Yan sandan sunce wadanda ake zargin, Chidozie Onyebuchi, mai shekaru 39, da Ifeanyi Odo, mai shekaru 42, sun sanar da jami'an 'yan sanda na SARS cewa wasu daga cikin wasu daga cikin shugabannin kasuwan ne suke biyansu duk wata, su kuma rika zuwa suna ladabtar da duk wani wanda yayi kokarin kalubalantar shugabannin a kasuwar.

Shugabannin kasuwa ne suke biyanmu mu fasa shagunan abokanan sana'arsu muyi musu sata - Cewar wasu barayi
Shugabannin kasuwa ne suke biyanmu mu fasa shagunan abokanan sana'arsu muyi musu sata - Cewar wasu barayi
Asali: Facebook

Onyebuchi da Odo sun bayyana cewa sun fara sana'ar ta su a matsayin barayi ne, inda har suka kai mawar da suka koma fashi da makami.

Onyebuchi, wadanda aka gabatar dashi tare da Odo da wasu masu laifin kimanin 300 a helkwatar 'yan sanda dake Ikeja a jiya Alhamis, ya ce: "Ni na fara a matsayin barawo ne a cikin kasuwa a shekarar 2015, daga baya na canja na zama cikakken dan fashi da makami bayan na hadu da Ifeanyi. Muna bacci a cikin kasuwar. Haka yasa muka gano yadda muke shiga cikin shagunan mutane da daddare.

KU KARANTA: An kama bakin haure guda 3 da suke shigowa da 'yan ta'addar Najeriya makamai

"Mun fi shiga shagunan sayar da kayan wuta. Sai mu sayar da kayan ga wasu 'yan kasuwar dake wajen kasuwar."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, wanda ya gabatar da masu laifin, ya bayyana cewa a ranar 4 ga watan Agustan shekarar 2020, SARS sun kama Onyebuchi da Odo sun shiga shagunan wasu a kasuwar Alaba, inda suka saci kayayyaki na miliyoyin nairori.

Abubuwan da aka samu a wajen su sun hada da talabijin mai girman inci 32 kirar LG, da sauran abubuwa da suka sata a shagunan mutane. Sun amsa laifinsu na cewa suna wannan sana'ar tasu sama da shekara uku.

Ana cigaba da gabatar da bincike akan su, inda daga baya za a mika su kotu da zarar an kammala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel