Babangida Aliyu: Bayan sa’o’i, an rusa dakatarwar da aka yi wa Jigon PDP saboda Jonathan

Babangida Aliyu: Bayan sa’o’i, an rusa dakatarwar da aka yi wa Jigon PDP saboda Jonathan

- Shugabannin PDP sun ce batun dakatar da Muazu Babangida Aliyu ba gaskiya ba ne

- PDP ta reshen jihar Neja ta ce ta dakatar da tsohon Gwamna, Dr. Babangida Aliyu

- Shugabannin Jam’iyya na shiyyar Arewa maso gabas sun ce Aliyu ya na nan daram

Shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso tsakiya da ke kula da jihar Neja, sun soke dakatarwar da aka yi wa Muazu Babangida Aliyu.

A cewar jaridar Punch, kwamitin na rikon kwarya ya fitar da jawabi ta bakin sakataren yada labarai, Suleiman Mohammed, a game da lamarin a ranar Litinin.

Malam Suleiman Mohammed ya ce labarin cewa an dakatar da tsohon gwamna, Dr. Muazu Babangida Aliyu daga jam’iyyar PDP mai adawa, ba gaskiya ba ne.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Tsohon Gwamna Babangida Aliyu

Shugabannin riko na yankin Arewa ta tsakiya sun yi watsi da matakin da reshen PDP na Neja ta dauka, su ka ce har yanzu tsohon gwamnan ya na a jam’iyyar PDP.

Ya ce: “Ya zo mana cewa wani labarin bogi ya na yawo a kafafen sadarwa na zamani cewa an dakatar da tsohon gwamnan Neja, kuma daya daga cikin ‘yan BOT.”

“Duk da mu na ganin babu amfanin maida martani ga masu yada labaran bogi a dandalin sada zumunta, mu na ganin akwai bukatar a fadi gaskiyar abin da ya faru, saboda gudun a rudar da dinbin mabiyanmu da ke jihar Neja da wasu wuraren.” Inji Sulaiman.

“Maganar ita ce Babangida Aliyu, tsohon gwamna ne wanda ya na cikin majalisar amintattu da ta zartarwa, don haka reshen PDP ta gida ba za a iya dakatar da shi ba.”

Babaginda Aliyu: Bayan sa’o’i, an rusa dakatarwar da aka yi wa Jigon PDP saboda Jonathan
Dr. Muazu Babangida Aliyu Hoto: guardian.ng

KU KARANTA: Amaechi ya ce akwai bukatar a rika damawa da mata a Gwamnati

“Masu yada wannan labari na bogi, makiyan PDP ne, wadanda su ke kokarin jawo rabuwar kai.”

“Mu na kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarmu da sauran jama’a su yi watsi da wannan labari wanda aikin magauta ne. Mu na kira ga PDP a Neja su hada-kai, a kai ga nasara.”

A jiya kun ji labarin cewa babban jagoran Kwankwasiyya, kuma jigon adawa a Kano, Aminu Gwarzoya caccaki shirya bikin Tinubu a Kano, ya ce akwai lauje a nadi.

Aminu Gwarzo ya ce babu abin da ya hada taron da aka yi da yunkurin hada-kan kasa ganin yadda Bola Tinubu ya yi gum a lokacin da ake hallaka mutane a Ibadan.

Source: Legit.ng

Online view pixel